Hukumar Gudanarwar Jami’ar Edo mallakin gwamnatin jihar, Ambrose Alli University (AAU), Ekpoma, ta kori ma’aikata guda biyar yayin da wasu 21 suke kan fuskantar bincike kan zargin aikata manyan laifuka daban-daban.
Mamba a kwamitin musamman (SIT), Austin Osakure, yayin da ke mika rahoton ayyukan SIT ga gwamna Godwin Obaseki a gidan gwamnati da ke Benin, ya shaida cewar ma’aikatan an koresu ne bisa la’akari da rahoton kwamitin da’a da ladaftarwa ta jami’ar.
Osakure, ya bukaci gwamnatin Edo da ta kafa majalisar koli ta gudanarwar jami’ar AAU, tare da daukan manyan jami’ai na jami’ar, ya lura kan cewa zuwa yanzu ba a yabawa ko gamsuwa da ayyukan kwamitin SIT, sai ya ce, ko kuma a sabunta ko yin nazari kan dokokin jami’ar domin kyautata lamuranta.
Ya shaida cewar jami’ar AAU ta bi umarnin gwamnatin jihar Edo wajen shiga cikin taimakekeniyar kiwon lafiya da ya fara aiki a ranar 1 ga watan Agustan 2023.
Mamban ya ce, “Dukkanin ma’aikatan jami’ar AAU da suke da sauran shekaru bakwai su kammala aiki an barsu ba su cikin shirin.
“Tsarin inshuran kiwon lafiya ta Edo na gudana yadda ya dace saboda ana biyan kudin ne kai tsaye ta asusun EdoHIS, domin tabbatar da gaskiya da adalci.
“Dalibai 998 sun shiga shirin, da sama da naira miliyan 15, da kuma ma’aikata 1,800 da sama da naira miliyan 31.
“Jami’ar ta gano kesa-kesai sama da 30 na dalibai ‘yan kasashen waje a cikin shekaru kasa da biyu, sun zana jarabawa har ma an yayesu. Ma’aikata da shugabannin tsangayoyin da suke da hannu a wannan lamarin an mika su ga jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ICPC domin daukan mataki na gaba.”
Mamban ya bayyana wa gwamnan cewar akwai tsare-tsare da dama wadanda suke tafiya a jami’ar da suke bukatar gaggawan kawo dauki da sauyi domin bunkasa harkokin jami’ar.
A jawabinsa, gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya ce, gwamnatinsa za ta tabbatar da dawo da martaba da kimar jami’ar AAU, kuma nan kusa za a samu sauye-sauye masu matukar fa’ida.
Obaseki ya ce, “Muna son mu magance matsalolin makarantar,” ya tabbatar.