Ana zargin cewa an kashe tsohowar shugaban kotun gargajiya ta jihar Benue, Misis Margaret Igbeta a gidanta da ke layin Wantor Kwange a cikin garin Makurdi.
Igbeta mai shekara 72 a duniya an tsinci gawarta kwance cikin jini a daren ranar Alhamis.
- Shugabannin Sin Da Afirka Sun Yi Tattaunawa Kan Zamanintar Da Kasa
- Firimiyar Bana:Wasanni Uku Da Za Su Fi Daukar Hankalin Masu Kallo
Rahotonni sun cewa an gano gawar mamaciyar ne a ranar Juma’a da safiya bayan da makasanta da har yanzu ba a san ko su waye ba suka aiwatar da aika-aikar nasu.
‘Yansanda sun dauko gawarta daga gidanta da ke kusa da kwalejin BSU a kan layin Gboko a Makurdi.
Majiya daga bangaren ‘yansanda ta shaida wa ‘yan jarida cewa, “Eh gaskiya ne a jiya (Ranar Alhamis) an tsinci gawarta a cikin gidanta.”
Majiyar ya kara da cewa ‘yansanda suna ta kokarin yadda za a bi wajen cafko makasanta tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Da aka tuntubi kakakin ‘yansandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce za ta binciki hakikanin abun da ya faru kafin bayyana wa ‘yan jarida.