Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya sake caccaki takardun makarantar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Atiku ya kalubalanci sahihancin takardar shaidar digirin Tinubu da jami’ar Chicago ta Amurka ta bayar, ya ce karatun shugaban kasar na ci gaba da zama babbar abun tantama.
- Sakaci: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Asibitin Hasiya Bayero
- Tottenham Da Chelsea Na Zawarcin Ansu Fati Na Barcelona
A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Tuwita, Atiku ya zargi shugaban kasar da kaurace kawo takardun karatunsa na firamare da sakandare amma sai ya kawo na digiri daga jami’ar Chicago.
A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, a shekarar 1999, Tinubu ya yi ikirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John’s da ke Aroloya a Legas, kafin ya wuce makarantar ‘Children’s Home’ da ke Ibadan.
Ya yi zargin cewa shaidar karatun Shugaba Tinubu a 2023 ya sha bamban da wanda aka gabatar a shekarar 1999, inda ya kara da cewa shugaban kasar ya ce ya halarci jami’ar Chicago ba tare da karatun firamare da sakandare ba.
“Na farka da safiyar yau ina mamakin yadda muka sami wannan lamari. A cikin 1999, Tinubu ya yi ikirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John da ke Aroloya a Legas, kafin ya wuce zuwa makarantar ‘Children Home’ a Ibadan.”
“A cewarsa, ci gaba da karatu kwalejin gwamnati ta Ibadan da kwalejin Richard Daley da jami’ar Chicago ta Amurka.
“Abin mamakin shi ne, a 2023, Tinubu ya ce shi dai kwai ya halarci jami’ar Chicago kadai. Ina ta mamakin ko ta yaya hakan zai yiwu? Yana tunanin cewa ’yan Nijeriya ba za su shiga rudani ba kamar yadda na shiga cewa, Tinubu ba shi da takardar firamare da sakandare amma ya yi digiri a jami’a. Kuna iya tambayar Tinubu yadda ya samu wannan nasarar domin mu yi koyi da hazakarsa,” Atiku ya rubuta.
A watan Maris ne aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023. Amma Atiku ya ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, inda ya kalubalanci sahihancin takardun makarantar shugaban kasa.
Ya kuma garzaya wata kotun Amurka da ke gundumar Arewacin Jihar Illinois a Chicago, domin neman tilastawa jami’ar Chicago sakin bayanan karatun Tinubu.