An yi kira ga Sarakuna Gargajiya a yankin karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina da su tabbatar jama’arsu da suka cancanci karbar katin zabe sun karba a cigaba da rajista da ake a halin yanzu.
Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello, ya bayar da wannan umarnin a lokacin da jami’in hukumnar zabe na karamar hukumar, Malam Yunusa Abdu ya kai masa ziyarar bangirma a fadarsa da ke Kankara.
- Wata Kungiya Ta Bukaci Zaurawa Da Su Rungumi Sana’o’in Dogaro Da Kai
- Hukumar Kashe Gobara A Jihar Kano Ta Ceto Mutum 135 A Watan Yuni
Ya kuma nemi al’umma yankin su yi amfani da wannan karin wa’adin da aka yi wajen karbar katin zabe da ke tafe a 2023.
Hakimin wanda kuma shi ne kuma Kanwan Katsina, ya bayyana muhimmancin katin zaben, inda ya ce, da ita ce mutum zai iya sauke nauyin da tsarin mulki ya dora masa na zaban shugabanni a wannan lokacin.
A jawabinsa tunda farko, shugaban hukumar zabe na karamar hukumar, Malam Abdu ya bayhana cewa, ya kawo ziyarar ne don sanar da Haikimin cewa, a halin yazu sun samu karin na’urar yin rajista daga ofishin hukumar da ke Abuja.
Ya ce, karin na’urar zai taimaka rage cunkoson da ake fuskanta wajen yi wa al’umma rajista a yankin.
Kauyukan da ake gudanar da rajistar sun hada da Ketare, Hurya, Tsamiyar Jino, Kuka Sheka, Gundawa, Tudu, Gurbi, Katoge da kuma Pawwa.
Ya kuma yaba wa sarakuna gargajiya a kan irin gudummwar da suke ba hukumar.