Hedikwatar rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta sanar da cewa, ta cafke wasu dalibai guda uku da wani mutum daya bisa zarginsu da kasance cikin kungiyar asiri mai suna Black axe.
Wadanda aka kama bisa wannan zargin, su ne, Eric Nuhu mai shekara 23 – dalibi ne da ke matakin karshe a jami’ar ATBU da ke Bauchi; Zaharaddeen Hassan, dan shekara 19, da ke matakin karatu (ND 1) a kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Bauchi; Felix John dan shekara 24 – dalibin karatu da ke (HND 1) a kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya da ke Bauchi; da kuma wani mai suna Daniel Masaka dan karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
A sanarwar manema labarai da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Muhammad Wakil ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, a bisa binciken da suka yi, sun gano cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin na farko da na biyu sun bayyana cewa, wani abokin karatunsu ne, Abbas Apeh da ke matakin karshe a jami’ar ATBU Bauchi ne ya gayyace su shiga cikin kungiyar a ranar 2 ga watan Satumban 2023.
Sauran kuma da ake zargin, sun tabbatar da cewa sun jima da kasancewa mambobin kungiyar asirin ta Black axe.
Ya ce, mambobin kungiyar ne suka gayyacesu domin su halarci wani bikin tarbar amsar sabbin mambobi da aka gudanar a wani waje a Bauchi da ke kusa da matsugunin jami’ar ATBU na dindindin da ke Gubi a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Kano.
Kazalika, a wani labarin makamancin wannan, rundunar ta kuma kama wasu mutum biyu da suka kasance kwararru a bangaren kwacen mashina kuma sun shafe sama da shekaru hudu suna tsula tsiyarsu a cikin kwaryar Bauchi da jihohin makwafta.
A ranar 24 ga watan Agustan, wani mutum mai suna one Aliyu Muhammad Gidado mazaunin unguwar tsohowar Airport inda ya kai rahoto ga ‘yansanda cewa a wannan ranar ya gano wani Bello Mohammed da aka fi sani da Faruk Manja dan shekara 30 mazaunin unguwar Bakaro shi da wani mai suna Kabiru Danfulani da ke Muda Lawal Bauchi (da yanzu ake nema) sun shiga cikin gidansa tare da sace masa mota kirar Honda Civic mai lamba MSA-350-PD da kudinta ya kai naira N640,000;00 tare da wata kwarangwal din mashin hadi da wasu kadarorin da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.
Wakil ya ce bayan da suka kaddamar da bincike sun kamo wanda ake zargi da kuma abubuwan da suka sace a lokacin da suke kokarin arcewa.
A cewarsa a lokacin bincike wanda ake zargi na farko ya ce, ya shafe shekaru hudu yana satar mashina kuma zuwa yanzu ya sace mashina za su kai 20 a jihohin Bauchi da Yobe. yayin da shi kuma wanda ake zargi na biyun ya gudu.
Sanarwar ta ce za su gudanar da wadanda suke zargin a gaban kotu da zarar suka kammala gudanar da bincike.