Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra sun kama wata mata mai shekara 29 bisa zargin sace wata yarinya ‘yar shekara uku.
Wadda ake zargin, Miss Chinwendu Umegbaka, a cewar kakakin ‘yan sandan, DSP Ikenga Tochukwu, ta fito ne daga Isinkwo Abaomege a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Hana Hakar Ma’adanai
- Mun Shirya Tsaf Don Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihar Osun —INEC
Kakakin ‘yan sandan ya ce a ranar Asabar 2 ga watan Yulin 2022 da misalin karfe 4:30 na yamma a titin Nwawulu, Okpoko a Onitsha, ana zarginta da sace yarinyar makwabcinta ‘yar shekara uku da niyyar sayar da ita domin samun kudi.
Toochukwu ya shaidawa manema labarai a jiya cewa an kubutar da yarinyar da abun ya shafa kuma an mayar da ita ga iyayenta.
Ya ce: “Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a ranar Asabar, 2 ga Yuli, 2022, da karfe 4:30 na yamma sun kama wata Miss Chinwendu Umegbaka, ‘yar shekara 29, ‘yar asalin Isinkwo Abaomege a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.
“An kama ta ne bisa zargin satar wata yarinya a titin Nwawulu, Okpoko, Onitsha, jihar Anambra.
“Bincike na farko ya nuna cewa wadda ake zargin makwabciyar ce ga iyayen yarinyar.
“Da farko an kama Chinwendu amma ta musanta cewa ta san inda yarinyar ‘yar shekara uku take. Karin tambayoyin da ‘yan sandan suka yi mata ya sa ta amsa laifin satar yarinyar da nufin sayar da ita.”
A halin da ake ciki, an gano yarinyar kuma an mika ta ga iyayen,” in ji Ikenga.