Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima.
Ya ce duk da cewa dokar zabe ta Nijeriya ita ce mafi inganci a tarihin kasar, amma ba ta cika ba; kuma akwai bukatar a kara yin gyare-gyare don kawar da shubuha da kuma karfafa wasu sassanta.
- Sin Ta Yi Rawar Gani Wajen Ingiza Ci Gaban Duniya Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
- Wakilin Sin A MDD Ya Yi Kira Da A Aiwatar Da Matakan Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta Tsakanin Falasdinu Da Isara’ila
Ya bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu da cibiyar nazarin harkokin dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya wa sanatoci a garin Ikot Ekpene, jihar Akwa Ibom.
Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata a gyara hanyar lantarki daga zabuka masu zuwa a shekarar 2027.
Ya kuma ce, bai kamata shugaban kasa ya sake samun ikon nada shugaban INEC da kwamishinonin hukumar na kasa ba domin kwato hukumar daga bangaranci.
Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da cewa an warware duk wasu batutuwan da suka taso a kan gudanar da zabe tare da yanke hukunci kafin ranar da za a rantsar da su.
Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda sashe na 64 na dokar zabe, wanda ya bayyana yadda ake yada sakamakon zaben, na da saukin magudi.
Sai dai Jega ya ce ya kamata a fayyace sashen ta hanyar wajabta watsa sakamakon zabe, gami da dora sakamakon matakin zabe da takardar sakamakon da ake amfani da shi a matakai daban-daban na tattara sakamakon zabe.
“INEC za ta samu isasshen lokacin da za ta shirya aiwatar da wannan, idan an yi wa dokar kwaskwarima da wuri a zaben da ke tafe,” in ji shi.
Ya kuma yi kira da a bullo da yanayin fara kada kuri’a ga wadanda suka cancanci kada kuri’a, kamar ma’aikatan INEC, masu sa ido da direbobinsu, jami’an tsaro, da ‘yan jarida ko kuma wani tsari na musamman da zai ba su damar kada kuri’a a ranar zabe, musamman zaben shugaban kasa.
Tsohon shugaban na INEC ya bayar da shawarar cewa ‘yan kasashen waje su kada kuri’a, musammam zaben shugaban kasa, don bai wa ‘yan kasa damar kada kuri’a, musamman wadanda ke aiki a kasashen waje.
Ya ce, “Akwai bukatar a sanya tsauraran sharudan janyewar dan takara da kuma maye gurbinsa don hana cin zarafi. Ba wa INEC damar tantancewa da kuma idan ya cancanta ta haramta wa ‘yan takarar da shaidarsu ta nuna cewa ba su cancanta ba.
“Akwai bukatar doka ta ba wa ‘yan takara da ke wajen jam’iyyun siyasa dama, da kuma ‘yan kasa masu biyan haraji su shigar da kara a kan ‘yan takarar da ke bai wa INEC bayanan karya game da takararsu.
“Duk da cewa sashe na 132(8) & (9) ya bayar da wa’adin da kotuna da kotunan daukaka kara za su yanke hukunci, akwai bukatar musamman dangane da zababbun mukaman zartarwa, a tabbatar da an warware dukkan shari’o’i da kuma yanke hukunci a gabanin. ranar rantsuwa.
“Bincika tsarin nade-naden mukamai a INEC, musamman don karfin shugaban kasa wajen nada shugaban INEC da kwamishinonin INEC na kasa, domin kubutar da hukumar daga mummunan zato da ake maga.
“Ya kamata a samar da ka’idoji don gabatar da koke-koke ga duk wanda aka zaba yayin wannan aikin.”