Mambobin kungiyoyin kwadago da suka hada NLC da TUC sun tare hanyar zuwa titin filin jirgin saman Abuja, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa masu zanga-zangar na neman a soke zirga-zirgar jiragen da za su je Owerri, babban birnin jihar Imo a wani mataki na ganin an tabbatar da biyan hakkin ma’aikata a jihar biyo bayan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero, da ‘yansanda suka yi.
- Taron MDD: Gwamntin Tarayya Za Ta Dauki Nauyin Gudanar Da Makarantar UNESCO A Nijeriya – Minista
- Ba Mu Janye Tsofaffin Takardun Naira Ba – CBN
Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna John, ya ce hakan na daga cikin jerin abubuwan da kungiyoyin za su don nuna bacin ransu kan harin da aka kai wa shugaban NLC.
A halin da ake ciki, wani ma’aikaci a filin jirgin, Christopher Wilson, yayin da yake tabbatar da zanga-zangar.
“Sun tare hanyoyin shiga da fita na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.”
Ya kuma ce mambobin kungiyoyin kwadagon sun taru a filin jirgin ne tun da misalin karfe 8:58 na safe domin aiwatar da umarnin da suka ba mambobin da ke aiki a bangaren sufurin jiragen sama na dakatar da tashin duk wani jirgi mai zuwa filin jirgin Sam Mbakwe Cargo da ke Owerri.
Masu zanga-zangar sun yi yunkurin shiga filin jirgin amma jami’an soji da ke shingen binciken suka hana su.
Idan za a tuna cewa NLC da TUC sun shelanta yajin aiki a fadin kasar nan, wanda zai fara aiki a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, domin nuna adawa ga gwamnatin jihar Imo.