Samin kowa ne wannan abin ba ya tsaya kadai bane kan Maigida domin halin da ke ciki na rayuwar yau da kullun, duk dan Adam yana ji a jikinsa,musamman ma yadda tabarbarewar darajarNaira ta shafi abubuwan da ake saye da sayarwa a kasuwanni Kauyuka da Biranan Nijeriya.
Maganar tsadar kayayyaki wadanda sun kunshi na cin yau da kullun da dai sauransu.
Da yake ana gab da yin babbar Sallah wadda cikin ikonAllah zata kasance ranarAsabar,saye kayayyakin da za ayi amfani da su ranar Sallah,manyan daga cikinsu sun hada da na farko shi ne abincin da za a dafawa a ranar Sallah.Suturar ko kayan da za a yi amfani dasu,sai uwa uba kuma akwai sayen maganar Ragon Layya wadda ta kasance ba dole bane sai idan mutum yana da halin yi.
Baidace ba idan Maigida ya san bai da wani hali na yin Layya ya matsa ma kan shi cewa sai ya amso bashin kudi daga wani wuri ya je ya sayi Rago,wani ma yana yin hakan ne domin ya burge makwabtansa ko iyalansa,bayan Sallah kuma a shiga yin tsulla- tsulla idan lokacin da aka tsaida na biyan bashin ya yi.
Masu iya magana sun ce mai daki shi ne ya san inda ruwa ke zubar ma sa don haka ne, ya dace ya tafiyar da al’amuransa daidai ruwa daidai tsaki.Ko kuma daidai ruwa daidai kurgi.Shi ya san yadda aljihunsa yake, bai kamata ya amince da duk wata shawara wadda daga karshe zata wahalar da shi ba, ko domin ya burge wasu ba ace shi ma mai hali ne.
Bayankuwa abin duk wani karfin hali ne wanda zai sa kansa yi na babu gaira ba dalili.