Hukumar kula da al’amuran ilmi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa Afirka na bukatar Malaman makaranta a kalla milyan 15 da za su koyar a makarantun Sakandare na da shekara ta 2030.
Ya ce Afirka na fama da karancin Malaman makaranta a makarantu masu yawa al’amari ya kasance haka ne saboda rashin isassun kudaden da ake ware ma sashen ilimi a shekarun da suka gabata.Ya ci gaba da bayanin cewa duk da cigaban da aka samu akan daukar Malaman makaranta shekaru biyar da suka wuce a nahiyar amma ya ce al’amarin ya hadu da tafiyar Hawainiya don haka ya yi kira da gwamnatocin Afirka Kudu da Sahara su kara yawan Malaman makarantar da suke dauka ko wace shekara.
- Abubuwan Da Nijeriya Za Ta Mora Daga Taron Saudiyya Da Jamus
- Kayan Tarihi Na Manzon Allah S.A.W (II)
Babban mai sharhi kan harkokin ilimi a UNESCO,Patrick Nkengne,ne ya bayyana Malaman makaranta ‘yan kadan ne suke kula da milyoyin dalibai a nahiyar Afirka.
Ya ci gaba da bayanin “Lokacin da ajin da ya dace da dalibai 50 amma sai aka samu 100, tun tashin farko an fi son Malamin makaranta daya ya kula da dalibai 40 zuwa 50 abin da doka tafi amincewa da shi ke nan,amma a fili abin ya nuna da akwai matsala.Yayin da ake cigaba da samu karancin azuzuwa matsalar rashi ta karu ke nan cewar Nkengne,”.
Ilimin da ya shafi Sakandaren da akwai bukatar Malaman makaranta da yawa a yawancin kasashen Afirka.Emmanuel Manyasa shi ma kwararre ta harkar ilimi ya ce makarantu da yawa suna yaye daliban da basu da ilimi ne saboda rashin kwararrun Malaman makaranta.
“Wannan ya nuna da akwai Malamai wadanda basu jin dadi tsanin saboda su kansu da kuma masu koyo.
Masu koyo basu samun kulawar da ta kamata su samu,ya yin da su Malaman makaranta yawan daliban da suke kulawa da su ya dame su da yawan awoyin da suke dauka na koyarwa wanda hakan bai basu dama ta shirya abubuwan da za su koya wa dalibai.Shi yasa suke zuwa aji ba tare da sun shirya ba tare da danne wata dama data kamata su samu.Daga karshe sai makarantu su zama wurin zuwa a koya ba tare da karuwa da ilimin daya dace a samu ba.”
Kamar yadda Nkengne ya ce a kasashen da suke da isassun Malaman makaranta su makarantun ne suke kokarin bada ilimi mai nagarta ka wadanda suke koyo saboda rashin samun kyakkyawan farawa ta ilimin da ya dace a fara sani.
“Abu mafi dacewa shi ne ace Malamin makaranta ya samu shirin yadda zai fuskanci dalibai wajen koya masuIn saboda hakan za isa su karu da ilimi mai inganci.Sai dai kash! Kuma wadanda za su koyar din basu samu kwarewa akan darussan da suka kamata su koyar.
“A irin wannan yanayin ba yadda za ayi su daliban su koyi wani abin azo a gani saboda basu da Malami,wannan abin yana da wuyar ganewa idan ana bukatar yin hakan abu mafi dacewa shi ne su Malaman ya dace ay masu jarabawa da tabbatar da sun samu nasarar data su koyar.”
Manyasa ya ce ya kamata a karfafawa Malaman makaranta gwiwa domin hakan zai sa su maida hankali wajen ganin an cimma burin da ake bukata.
Ya kara jaddada cewa “Ya kamata mu tabbatar da ana kai Malaman makaranta wuraren da suka kamata a fadin kasa.Ta haka ne ake gane me ya dace ayi yaya za ayi shi na jan hakalin su Malaman su yi aiki a wuraren da basu taba tunanin za su je ba.
Yawancinsu ba su shirya ma wurin da yanayin shi basu saba da shi ba ga kuma al’amarin da ya shafi rashin tsaro,ko zuwa kauye su yi aiki,ai zai yi wuyar a shawo kan irin kan wadancan Malaman su je su yi aiki a irin wadancan wuraren? Ai wannan al’amari ne mai muhimmanci.”
Masu ruwa da tsaki shi yasa suka ja hankalin gwamnatocin Afirka su duba ko tunanin Malaman makaranta nawa za a bukata nan dka shekaru goma masu zuwa,ga kuma duba yadda za a rika horar da su,da samar da kudade saboda daukar Malamn tare da horar da su.