Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) na taka muhimmiyar rawa wajen bayar da tallafi da taimako ga kasashen da suke fuskantar matsalolin tattalin arziki. Amma bashin IMF na iya zama matsala ga kasashen da suka karba musamman ga tattalin arzikinsu saboda tsauraran ka’idoji da hukumar kan gindaya wa kasashen da suke karbar basukan musammnan kasashen yankin Afirika inda ake fama da matsanancin talauci.
Mujallar ‘Business Insider Africa’ ta binciko tare da kawo muku kasashe 10 na Afirika da suka fi kowace kasa dakon bashin IMF.
- An Cimma Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Mai Ma’anar Tarihi
- CITAD Ta Horar Da Matasa 40 Kan Fasaha A Kano
Yawancin kasashen da suke rungumar basukan IMF suna yi ne yayin da suka shiga matsalar karayar tattalin arziki, basukan ya kan taimaka musu wajen rage radadin da matsalar tattalin arzikin ke haifarwa.
Basukan ya kan taimaka wa kasashen tafiyar da harkokinsu har sai abubuwa sun daidata, haka kuma basukan yana taimakawa wajen daga mutuncin kasashe a idon duniya, yadda kasa ta yi kokarin biyan basukan yana taimakwa wajen kara samun wasu tallafi daga cibiyon bayar da tallafi na duniya.
A nan kuma mun kawo muku kasashe Afirka 10 da suka fi kawacce kasa yawan bashi daga IMF kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na intane a ranar 6 ga watan Disamba 2023.
Kasashen sun hada da 1. Masar da ke da bashin Dala 11,968,321,674 2. Angola mai bashin Dala 3,153,816,667. 3. Afirika ta Kudu nada bashin Dala 2,669,800,000. 4. Côte d’Iboire nada bashin Dala 2,117,559,620 5. Kenya nada bashin Dala 2,058,982,100, 6. Nijeriya na dakon bashin Dala 1,840,875,000 7. Ghana Dala 1,644,377,000 8. Morocco Dala 1,499,800,000 9. Jaumhoriyyar Kongo, Dala 1,294,500,000 sai kuma na 10. Tunisia da ake bi Dala 1,259,139,338.