A tattaunawar da aka yi tsakanin manyan ‘yan jaridu, Shu’aibu Mungadi, Salihu Dantata, Ibrahim Gamawa, bisa jagorancin Aminu a gidan talabijin na Farin wada da Rediyon Bision, sun tabo al’amuran yau da kullum, da suke addabar Nijeriya, wadanda suka jefa ‘yan kasar cikin wahalhalu, kamar maganar tallafin mai da kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati, kalubalen rashin tsaro da sauransu.
Wakilimu ABUBAKAR ABBA ya saurari tattaunawar kuma ya rubuto mana bisa gudunmawar marigayi Shugaban Matasan Arewa Mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci, kamar haka:
- Harin Filato: Gwamnati Ba Za Ta Huta Ba Har Sai An Hukunta Maharan – Shettima
- Gwamnan Katsina Ya Yi Wa Ma’aikatan Jihar Ƙarin ₦10,000 Kan Albashi, ‘Yan Fansho ₦5,000
Batun tallafin mai….
Abu ne wanda tun gwamnonin da suka gabata, an sha samun matsalolin ware su bangare daya, inda za a yi handama da kudin da kuma jeka ka ji dadinka ba tare da an yi amfani da da su yadda ya kamata ba, wanda ya zamo abin da yake cutar da gwamnatin.
EFCC ta sha yin na ta kokarin, amma wasu lokutan, ba kwato kudaden ba ne saboda akwai wannan maganar ta dokar ‘yancin samun bayanai wanda wajibi ne wanda ya nemi wani bayani ko na menene aje a nuna masa. Kudaden nan da aka kwato, kafin wadannan me aka yi da su, koke-koke ko zarge-zargen cewa wadansu za su je kafafen yada labarai a zo a gaya mana an kwato daga bayan fage sai a je a yi almubazzanaranci da su.
To yanzu da suka kwato kudaden, sai ga shi Nijeriya ta je tana ranto kudi daga kasashe kamar su China wanda bai kamata ba. To menene mahimmancin kwato wadannan kudaden kuma ba ga wannan kudin tallafin kadai ba, wannan kwato kudin muna ji ne kawai a takarda ba a zahirance ba. Muna son a zo a gaya mana wadanda aka kwato a baya har da na yanzun me aka yi da su?