Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Alhamis din nan cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya, don ci gaba da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, da kara gudanar da ayyukan da za su amfani dukkan kasashe, da bayar da babbar gudummawa wajen inganta zamanantar da duniya da samar da ci gaba cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna da samun wadata tare.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya shekaru fiye da 10 da suka gabata, raya shawarar cikin hadin gwiwa ya fadada daga kasashen Turai da Asiya zuwa Afirka da Latin Amurka, tare da gina dandalin hadin gwiwar kasa da kasa mafi girma a duniya. Yayin da duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauye-sauye, mutane da yawa sun fahimci daraja da muhimmancin shawarar a duniya.(Ibrahim)