A Karamar Hukumar Nafada da ke Jihar Gombe, wata sabuwar cuta ta barke wacce ta yi sanadiyyar rasuwar matasa sama da 30 ‘yan kasa da shekara 20 a duniya. Lamarin, wanda ya yi matukar ta da hankalin al’ummar yankin, musamman kan yadda har zuwa yanzu ba a gano hakikanin wace irin cuta ba ce, ya fi shafar yara ‘yan makarantar sakandare.
Wakilinmu ya zanta da masu ruwa da tsaki inda suka nuna matukar damuwarsu a kan wannan cuta. Koda-yake, tun da farko an yi zargin cewa, cutar Sankarau ce amma bayan gwaje-gwajen da jami’an kiwon lafiya suka yi, an gano cewa ba ita ba ce, kuma har zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
Malam Yusuf Isa Jigawa, da ya rasa dansa mai shekara 17 a duniya, Abdul’aziz Yusuf Isa; dalibi a Makarantar CGSS Nafada, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, “Al’amarin nan, ya addabe mu a wannan yanki baki-daya. Mu dai a kashin kanmu, ba mu san wane irin ciwo ba ne kuma wannan ciwon idan ya samu yaro iyakar nisan zangonsa awa 24 ne, idan kuma ya wuce haka idan da rabo zai iya tashi. Amma mafi yawan su babu wanda ya wuce kwana guda”, in ji shi.
Da aka tambaye shi alamomin cutar, ya ce, “Ni dai nawa yaron ya fara kokawa kan cewa; kansa yana yi masa ciwo, daga maganar kansa na ciwo sai ya ce min kafarsa ma tana yi masa ciwo, daga kafa sai ya ce min cikinsa na ciwo, sai kuma kishirwa, yana bukatar ruwa a ba shi ruwa a ba shi ruwa, shi kenan sai aka ba shi ruwan, daga shan ruwa sai amai, bayan amai sai ya dan kwanta; jimawa kadan ya ce zai je bayan gida, amma ya kasa tashi. Duka-duka, wannan bai wuce awa guda ba ya kasa tashi, sai ni ne na dauke shi na kai shi.
“Bayan mun dawo, na tambaye shi cewa yanzu me yake ji? ya ce kafarsa yana ji kamar ana soka masa wutar lantarki. Bayan da muka ga abin ya wuce lissafi, sai muka dauke shi zuwa asibiti; nan ma ba abin da suka iya yi masa”, ya shaida.
Yusuf ya kara da cewa, jami’an kiwon lafiya sun yi gwaje-gwaje domin gano wace cuta ce, amma har yanzu ba a samu gano bakin zaren ba.
Malam Isa ya yi kira ga gwamnatoci da kungiyoyin kiwon lafiya da su kawo dauki zuwa wannan gari, domin dakile yaduwar wannan cuta.
Isa ya ce, a rana daya tak suna iya rasa yara sama da biyar, kuma kawo lokacin da aka zanta da shi babu wani rigakafin da jami’an kiwon lafiya suka yi musu, “Sannan, mafi yawan wadanda suka mutu matasa ne ‘yan kasa da shekara 22 zuwa kasa. Kazalika, an rasa yara sama da 50 a cikin kasa da wata biyu.” In ji shi.
Shi ma, Ali Bappa Alnafati, shugaban kungiyar bunkasa ci gaban Nafada, wanda shi ma ya rasa ‘yarsa mace, ya ce, babban abin da ke damunsu da ba a gano wace irin cuta ba ce da ke hallaka yara a wannan gari, wadanda mafi yawansu ‘yan sakandari ne.
“A yau da kuka same mu wurin amsar gaisuwar ta’aziyya, dan yayana mai suna Usmanu ne ya rasu. Ni ‘yata ita ce ta fara rasuwa wacce ta rasu a ranar 4 ga watan 2 na wannan shekara. Shi wannan ciwo ya yi nisa ne ya kai kwana biyu, idan ya kama yaro.
“Alamomin ciwon, sun hada da ciwon kai, ciwon kafa, idan yaro ya yi korafin ciwon kai to komai girmansa za a ga kafafunsa ba za su iya tafiya ba, sai an daga shi. Wadannan abubuwa su ne diyata ta yi fama da su, kuma ba ta kai awa 48 Allah ya karbi rayuwarta, haka sauran yaran ma. Haka shi ma wannan yaron Usman, ya ma yi hira da daddare lafiya kalau cikin dare ciwon ya kama shi, an fita za a kai shi asibiti da safe Allah ya karbi rayuwarsa.”
Kan adadin yaran da suka rasu ya ce, “Wallahi daga rasuwar ‘yata zuwa yau, mu je makabarta ba ku kirga ba za ku kirga yara 70 da suka rasu.”
A nasa bangaren, sakataren babban asibitin Karamar Hukumar Nafada, Kefas K. Sinna, ya bayyana cewa, “Gaskiya kam abu ya shigo mana kowa ma ya rasa meye ne ke tafiya. An fara kawo mana yaran nan da ciwon kafa da ciwon kai, ciwon kai din nan ma ba yadda za a kwatantashi da kuma ciwon ciki, wani lokacin kuma da amai.
“Mu a nan asibitin mutum bakwai ne muka yi recording din mutuwarsu, amma mafi yawa mutuwar kam a cikin gari ake yi. Daga farko mutum biyar ne daga baya kuma 2 suka karu a wannan asibitin. Tun daga nan kuma abun sai karuwa ya ke yi, ya yi sauki ya dawo ya yi sauki ya dawo.
“Likitoci sun yi aiki an dauki sample guda 20 an tura da tunanin cutar Sankarau ce, inda aka samu guda 11 ba cutar ba ce, yayin da muke cigaba da zaman jiran amsar guda tara,” sakataren asibitin ya tabbatar.
“Har yanzu ba a gano wacce irin cuta ba ce, sai dai muna bada shawarar kar a tsaya kan gwaje-gwajen cutar Sankarau zalla tun da ba a san menene musabbin ciwon ba. A dauki sample na jini, fitsari da na bayan gida a je a cigaba da bincike domin gano menene damuwar.’
Kefas ya tabbatar da cewa, likitoci na zuwa daga cikin Gombe su na kan aiki tukuru domin shawo kan cutar da neman mafita kan halin da ake ciki.
A zantawarsa da wakilinmu, Sarkin Nafada Dr. Muhammadu Dadum Hamza, ya yi kira ne ga al’ummar masarautarsa da a kowani lokaci su rika kai ‘ya’yansu zuwa asibiti domin tabbatar da an ba su agajin gaggawa a lokacin da suke cikin hali na rashin lafiya.
“An yi mace-mace kashi biyu. Na farko shi ne wadanda suka rasu a asibiti, akwai kuma wadanda suka rasa rayukansu a gida. A kuma bisa bayanan da muke samu wadanda suka rasu a gida sun fi wadanda suka rasu a asibiti yawa.”
“Maganar a zauna da marar lafiya a gida ba hanyace da take da kyau ba, asibiti shi ne gata kuma muna da asibiti. Don Allah don Annabi kada mutum ya zauna da marar lafiya a gida. Ba wai san rashin lafiyar ya tashi gagara sai a ce a je asibiti ba, tun da farkon abun ya kamata a je asibiti.”
Shi ma dan majalisar da ke wakiltar mazabar Nafada ta Arewa, Hon. Muhammad Tahir Dangaladiman Nafada, ya shaida ma wakilinmu cewa, tun lokacin da aka samu labarin cutar, ya je ya sanar da kwamishinan lafiya na jihar Gombe halin da ake ciki inda kwamishinan a cewarsa ya tura jami’ai domin a dauki gwaji domin gano wacce irin cuta ce ke damun mutane.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai gwamnatin jihar ba ta tabbatar da hakikanin cutar da ta barke ba.