Kungiyar Matasan Arewa (AYCF), ta caccaki tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, kan sukar takarar Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC ta yi.
Ta sanar da hakan ne a taronta na ranar Juma’a, wanda shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Yerima Shettima ya jagoranta – kungiyar ta ce babu wani zabin mataimakin shugaban kasa ga Tinubu fiye da Sanata Kashim Shettima, wanda dan kishin kasa ne.
- Gwamnatin Kano Ta Rufe Makarantun Kiwon Lafiya 26 Saboda Rashin Lasisi
- Zaben Osun: An Tsaurara Tsaro Gabanin Zaben Gwamna A Osun
“Kada wani ya mayar mana da dimokaradiyyarmu ta zama gidan masu tsattsauran ra’ayin addini,” in ji kungiyar matasan arewan.
Kungiyar, a cikin sanarwar a ranar Juma’a, ta ce Babachir da abokan tafiyarsa na bukatar zurfafaf tunani kan mafita ga kasar nan.
A satin da ya gabata ne, Babachir ya soki takarar Tinubu da Shettima a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023.
Tun bayan zabar da Shettima a matsayin wanda sai yi wa Tinubu takarar mataimaki aka shiga tsegunaguni kan takarar ta Musulmi biyu.