Kafar yada labarai ta Forbes ta bayyana sunayen wadanda suka zama attajirai mafiya arziki a Nijeriya a shekarar 2024. Su ne: Aliko Dangote, Mike Adenuga, Abdulsamad Rabiu, da Femi Otedola.
Kafar ta bayyana cewa Arzikin Dangote ya haura zuwa Dala biliyan 13.4, na Adenuga ya kai Dala biliyan 6.7, yayin da Abdulsalam Rabiu yake da Dala biliyan 5.2 shi kuma Otedola yake da dala biliyan 1.4.
- Yadda Dangote Ke Ciyar Da Mutum 10,000 Kullum A Kano Baya Ga Buhun Shinkafa Miliyan 1 Da Ya Raba
- Bata Gari Sun Daka Wa Motar BUA Wawa A Kan Hanyar Zariya
Aliko Dangote shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka kuma bakar fata mafi arziki a duniya, inda aka kiyasta kudinsa ya kai kusan dala biliyan 13.4 a shekarar 2024. Katafaren kasuwancinsa na rukunnan kamfanin Dangote Group, na daya daga cikin manyan kamfanoni masu zaman kansu a Nijeriya kuma kamfani mafi daraja a Afirka ta Yamma.
Shi kuwa Mike Adenuga hamshakin attajiri dan Nijeriya ya yi shuhura ne da Kamfaninsa na Globacom, kamfanin sadarwa na biyu mafi girma a Nijeriya wanda har ila yau yake da ressa a Ghana da Benin. Haka nan Mike yana da hannun jari a Bankin Ekuitorial Trust da kamfanin hakar mai na Conoil (wanda a da ake kira Consolidated Oil Company). Forbes ta kiyasta darajar arzikinsa ta kai dala biliyan 6.7 a 2024.
A bangaren Abdulsamad Rabiu, hamshakin attajirin kuma mai bayar da agaji kuwa, shi ne wanda ya kafa kuma yake shugabantar rukunin kamfanonin BUA Group, wadda ke maida hankali kan masana’antu, ababen more rayuwa, da noma da kuma samun kudaden shiga sama da dala biliyan 2.5.
Femi Otedola hamshakin dan kasuwa ne a Nijeriya wanda yake shugaban kamfanin Lantarki na Geregu Power Plc. Har ila yau, Otedola ne ya kafa Kamfanin mai na Zenon Petroleum and Gas Limited, kuma shi ne ya mallaki wasu kamfanoni da dama da suke hada-hadar jigilar kayayyaki, gidaje, da kudi. A baya-bayan nan ya zuba jari a fannin samar da wutar lantarki a wani bangare na ‘yantar da fannin a Nijeriya.
A cewar Forbes, shekara guda kenan da attajiran duniya, wadanda arzikinsu ke ci gaba da tabarbarewa yayin da kasuwannin hada-hadar hannayen jari na duniya ke cikin ka-ka-ni-ka-yi saboda rikicin siyasa, da hauhawar farashin kayayyaki.
“Kamar yadda yake a tsarin tattalin arziki gaba daya, an fi mayar da hankali ne wurin tattara bayanan kudi. Yanzu an sami jerin mutane 14 da ke cikin da’irar hamshakai da suka mallaki dala biliyan 100, da kuma wasu hamshakai da arzikinsu ya kai kirgen lambobi 12. Hakan ya kasance ne a kimanin shekara hudu da suka wuce. Wadannan suna daga cikin kalilan da suka taki sa’a, inda darajar arzikinsu ta kai dala tiriliyan 2 gaba daya, ma’ana kashi 0.5 cikin dari kacal na attajirai 2,781 na duniya da suka mallaki kashi 14 cikin dari na dukiyoyin attajiran da ke doron kasa”. In ji kafar a rahoton da ta fitar.
Kafar ta kuma bayyana cewa, a halin yanzu an samu karin attajirai fiye da lokutan baya, inda ake da 2,781, an samu karin 141 idan aka kwatanta da yawansu a bara. Arzikinsu ya kai akalla dala tiriliyan 14.2 wanda aka samu karin dala tiriliyan 2 a kan na 2023.
Rahoton kafar ya kuma ayyana cewa Bernard Arnault shi ne ya ci gaba da rike kambunsa na hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya. Attajirin mai kasuwancin kayan alatu dan kasar Faransa, an kiyasta yana da dala biliyan 233, inda ya samu karin dala biliyan 22 a kan abin da ya mallaka a 2023.
Amurka dai ita ce take da tarin hamshakan attajirai 813 wadanda arzikinsu ya kai dala tiriliyan 5.7, sai kasar Sin da take bi mata da yawan attajirai 473 da suka mallaki dala tiriliyan 1.7.