Gwamnatin Jihar Kwara, ta kaddamar da rabon kayan aikin gona ga manoma ‘yan asalin jihar su kimanin 2,019, inda ta gargade su a kan sayar da kayan da ta raba musu, domin amfanin kawunansu.
An gudanar da rabon wadannan kayan gona ne a garin Ilorin, wanda kuma yana daya daga cikin zango na uku na daukin aikin Fadama ‘CARES’ na gwamnatin jihar.
- CISLAC Ta Gudanar Da Taro A Kano Kan Canjin Yanayi A Nijeriya
- Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Mutane 12 Da Dukiyar Miliyan 130 A Kano
Wasu daga cikin kayan da aka raba wa manoman sun hada da, injinan ban ruwa da abincin kajin gidan gona da sauran makamantansu.
A yayin kaddamar da rabon kayan, Gwamnan Jihar AbdulRahman AbdulRazak ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta sama wa manoma wannan dauki ne, domin rage musu radadin tattalin arzikin da suke fuskanta tare kuma da yakar yunwa da talauci a daukacin fadin jihar baki-daya.
AbdulRahman ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta tabbatar da ci gba da bibiyar kayan, domin manoman da suka amfana su su yi amfani da su yadda ya dace ba tare da sun sayarwa mutane daban ba.
Gwamnan, wanda shugaban kwamitin shiri na Fadama a jihar, Mista Ishiak Olayinka Oloruko-Oba ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, ana sa ran aikin da manoman da suka amfana shi, zai taimakawa daukacin al’ummar jihar baki-daya.
A nasa jawabin tun da farko, jami’in shirin na ‘Fadama CARES’ na Jihar Kwara Fadama, Dakta Busari Toyin Isiaka ya bayyana cewa, shirin na daya daga cikin daukin annobar Korona da kuma kokarin sake farfado da tattalin arziki.
A cewar AbdulRahman, “A yau muna raba wa manoma su kimanin 2,019 wannan tallafi, inda ya kara da cewa, a shekarar 2022, manoma guda 6,561 ne suka amfana da shi, inda kuma manoma guda 8,020, suka fito a kashi na biyu.”
Daya daga cikin wadnda suka amfana da wadannan kayayyaki, akwai Kwamarade Jamiu Ahmed inda ya bayyana cewa, dukkanin daukacin wadannan kaya sun zo ne a kan gaba, inda kuma ya yi alkawarin yin amfani da kayan yadda ya dace.