Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
Maza suna da bambanci wajen abin da suke so, ba lallai ne abin da yake burge wannan shi ke burge wancen ba, saboda sabanin ra’ayi.
Tabbas, akwai abubuwan da kowanne maigida zai iya so daga wajen matarsa, ga wasu daga cikinsu:-
Tsafta: Mace mai tsafta duniya ce in ji matasa. Ba sai namiji ba, kowa yana son kusantar mutum mai tsafta har a sahun sallah.
Hakuri: Hakuri maganin zaman duniya in ji Bahaushe, duk matsala idan aka yi hakuri za a ga karshenta in sha Allahu.
Shagwaba: Mace mai shagwaba dadin zama gare ta, ko mai tsufan maigida, za ki iya yi masa shagwaba idan kina son ganin annuri a fuskarsa.
Kalaman soyayya: Girman kai ne yake sa mata da maza rashin fada wa junansu kalaman soyayya, idan ba ki fada masa ba, to za ki yi sha’awar kawarki idan kin ji ta fadawa maigidanta a gabanki.
Biyayya da iya girki: Ko mahaukaci ba ya son rashin biyayya shi ya sa yake biyo mutanen da suka tsokane shi. Girki mai dadi har kyauta zai sa maigida ya yi miki saboda abinci shi ne bukatar dan’Adam na farko.
Biyan bukata da iya hira: Na farkon ba sai na yi bayani ba. Iya hira yana sa maigida ya dinga marmarin ganin mace, kowacce mace za ta iya gane irin hirar da maigida yake so. Wani ya fi son a kawo masa hirar munafinci, wani yana son hirar karatu amma irin su sun fi karanci.
Damuwa da matsalolinsa: Ki dinga nuna damuwarki da halin da yake ciki na rashin dadi ko Matsala ce a kasuwa ko wajen aiki ko ta karatu, sannan ki zama mai kula da farin cikinsa duk abin da yake farin jiki a kai, ki nuna masa kin fishi jin dadin abin.
Tattali: Mace mai tattali alheri ce wacce kowanne maigida yake so.
Duk tsufansa, ki ce masa baby za ki sha mamaki, watakila ma a ranar zai fara doro yana yanga.