Kawo yanzu dai saura wasanni bakwai a kammala gasar Firimiya ta Ingila kuma za a iya cewa kungiyoyi uku ne a cikin kungiyoyi 20 za su iya lashe gasar ta bana da suka hada da Manchester City, wadda ta lashe gasar a kakar da ta gabata da Liberpool da kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wadda rabon ta da lashe gasar yau shekara 20 kenan.
A yadda jadawalin yake a yanzu, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ce ta daya da maki 71 sai Liberpool a mataki na biyu ita ma da maki 71, yayin da kuma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a mataki na uku da maki 70 duka bayan buga wasanni 31.
- ‘Yan Ta’adda Sun Yi Yunƙurin Ƙwace Iko Da Sakatariyar Jihar Oyo
- Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Daga Da Kaso 5% A Rubu’in Farko Na Bana
Sai dai a ragowar wasannin da suka rage za a fitar da kungiyar da za ta lashe gasar ta bana wadda ta zo da bazata musamman ganin irin kokarin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal take yi na ganin ta lashe gasar ta bana.
ARSENAL:
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi karfin da a wannan kakar za a iya cewa ta cancanta ta lashe gasar Firimiya ta Ingila duba da irin kokarin kungiyar da kuma wasannin da kungiyar ta lashe da kuma kokari da ta yi wajen doke manyan kungiyoyi irinsu Manchester City da Liberpool da Manchester United da kuma samun nasara a wasannin da a shekarun baya ba sa iya samun nasara.
Wasu suna ganin sayen dan wasa Declan Rice da Arsenal ta yi a farkon wannan kakar shi ne dalilin da ya sa kungiyar take kokari saboda tuni wasu sun fara bayyana cewa shi ne ya kamata a zaba a matsayin dan wasan da aka saya a bana wanda babu kamarsa.
Tabbas komawar Declan Rice kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta taimaka wa kungiyar tare kuma da kokarin da wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar irinsu William Saliba da Martin Ordegaard da Bukayo Saka suke yi.
Ana ganin matasan ‘yan wasan da suke cikin tawagar ‘yan wasan Arsenal su ne suka sanya kungiyar take tabuka abin a zo a gani, sannan kuma uwa-uba kociyan kungiyar, Mikel Arteta, wanda a baya ya taba yin aiki tare da Pep Guardiola a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kuma suka lashe kofuna tare.
Kawo yanzu kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai tana ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai inda ko a ranar Laraba sai da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen sai dai an cire Arsenal din a kofunan Carabao Cup da kuma gasar cin kofin kalubale ta FA da a yanzu aka kai matakin kusa da na karshe.
Amma dai duk da haka Arsenal ta ba wa mara da kunya kuma dole ne a ci gaba da saka su a cikin jerin kungiyoyi uku da za su iya lashe gasar cin kofin Firimiya saboda har yanzu babu kungiyar da ta samu nasara a kan Arsenal a wannan shekarar ta 2024 wanda hakan yake nuna irin bajintar da kungiyar ta yi.
Ragowar Wasannin da suka ragewa Arsenal:
Afrilu 14: Aston Billa (H) Afrilu 20: Wolbes (A) Afrilu 23: Chelsea (H) Afrilu 28: Tottenham (A) Mayu 4: Bournemouth (H) Mayu 11: Manchester United (A) Afrilu 19: Eberton (H)
A cikin jerin wasannin da suka ragewa kungiyar Arsenal akwai manyan wasanni da suka hada da wasa da Chelsea da Tottenham da kuma wasa na biyun karshe da za su kai ziyara filin wasa na Old Trafford domin kece raini da Manchester United.
Ana ganin idan har Arsenal ta iya samun nasara a wadannan wasannin tabbas za su iya lashe gasar ta bana, kuma karon farko tun bayan shekara 20 rabon da kungiyar ta lashe gasar Firimiyar Ingila.
LIBERPOOL
A ranar Lahadi ne aka tashi wasa canjaras, kwallo 2 da 2 tsakanin Liberpool da Manchester United yayin wasan da ya gudana a filin wasa na Old Trafford wato gidan United, karawar da ke matsayin guda cikin mafiya zafi da kungiyoyin biyu suka yi da juna a baya-bayan nan.
Liberpool din dai ta sha da kyar ne a karawar domin kuwa kasa da mintuna 10 kafin tashi daga wasa ne ta iya farke kwallo ta biyu bayan samun bugun fenariti, amma tun farko Liberpool ta zura kwallo ta hannun Luiz Diaz a minti na 23 kuma a haka ne aka tafi hutun tabin lokaci, sai dai kasa da mintuna 5 bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ne Manchester United ta farke kwallon ta hannun Bruno Fernandes a minti na 50 ta kuma kara ta biyu ta hannun Mainoo a minti na 67.
Duk da yadda Liberpool ta mamaye zagayen farko na wasan, yanayin yadda ta gaza katabus a zagaye na biyu ya bayar da mamaki da kuma sanya fargabar yiwuwar yaran na Jurgen Klopp su bar Old Trafford ba tare da maki ba gabanin bugun fenaritin da ta basu damar tashi wasa 2 da 2.
Sai dai har yanzu Liberpool na da maki kankankan ne tsakaninta da Arsenal wato kowacce na da maki 71 in ban da banbancin kwallaye, yayin da Manchester City da ke matsayin ta 3 ke da maki 70 bayan da kowannensu ya buga wasanni 31. Lashe gasar Firimiya a wajen kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ba sabon abu bane domin shekaru uku da suka gabata sun lashe gasar hakan ya sa akwai ‘yan wasa da dama a cikin kungiyar da suka taba lashe gasar ta Ingila.
Har ila yau, a kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, akwai kwararrun ‘yan wasa da suka hada da Mo Salah da Diaz da Darwin Nunez da kaftin din tawagar wato Birgil Ban Dijk wadanda duka kwararrun ‘yan wasa ne da suke taimakawa kungiyar ga kuma uwa-uba sababbin ‘yan wasan da kungiyar ta saya irinsu Szoboslai da Mc Allister da kuma Wataru Endo, duka sababbin ‘yan wasa ne da kungiyar ta saya a farkon wannan kakar ta bana kuma sune suke jagorantar kungiyar a yanzu musamman dan wasa Mc Allister, dan Argentina, wanda ya lashe kofin duniya a kasar Katar a shekara ta 2022.
Tuni kungiyar ta Liberpool ta lashe gasar cin kofin Karabao Cup bayan ta doke Chelsea a wasan karshe sannan kuma kungiyar ta Liberpool tana ci gaba da buga gasar cin kofin Europa League inda ta fafata da Atlanta, ga gasar Firimiya da kungiyar take neman lashewa, sai dai a kwanakin baya Manchester United ta doke ta daga gasar cin kofin kalubale na FA Cup, hakan yasa har yanzu Liberpool za ta iya lashe kofuna uku rigis a wannan kakar idan ta samu nasara.
Sannan ‘yan wasan kungiyar suna fatan yi wa kociyan kungiyar mai barin ado, Jurgen Klopp sallama mai kyau, a kwanakin baya ne dai kociyan dan asalin kasar Jamus ya bayyana cewa a karshen wannan kakar zai ajiye aikin koyar da Liberpool kuma tuni kungiyar ta fara tunanin neman wanda zai maye gurbinsa bayan da Dabi Alonso ya ce zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta Bayer Liberkusen.
Ragowar wasannin da suka ragewa Liberpool:
Afrilu 14: Crystal Palace (H) Afrilu 20: Fulham (A) Afrilu 24: Eberton (A) Afrilu 27: West Ham (A) Mayu 5: Tottenham (H) Mayu 11: Aston Billa (A) Mayu 19: Wolbes (H)
A cikin wasannin da suka ragewa Liberpool, akwai wasa tsakanin ta da Eberton, wasan hamayya, da wasa da Tottenham da Aston Billa da kuma wasa da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United. Idan har Liberpool suka lashe wadannan wasannin sannan kuma kungiyoyin Arsenal da Manchester City suka yi tuntube tabbas za a iya cewa
Liberpool za ta iya zama zakarar gasar Firimiyar Ingila.
MANCHESTER CITY
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce take rike da gasar Firimiya ta Ingila kuma na uku kenan da kungiyar ta lashe a jere, hakan ya sa ta karya tarihin abokiyar hamayyarta, Manchester United, wadda itama a baya ta taba lashe gasar sau uku a jere a baya.
Manchester City tana da kwararrun ‘yan wasan irinsu Kebin De Bryune, wanda a karshen makon daya gabata ya zura kwallo ta 100 a kungiyar, da Erling Haaland da Rodri da sauran manyan ‘yan wasan kungiyar wadanda suke taimaka wa mai koyarwa Pep Guardiola, wanda hakan ya sa ta zama zakaran gwajin dafi idan ana maganar karfi da kwarewa a gasar firmiya da ma gasar cin kofin zakarun Turai.
Tabbas Manchester City ta nuna bajinta a ‘yan shekarun nan kuma ya zama dole a jinjinawa mai koyarwa Pep Guardiola, wanda ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai, karo na farko a tarihin kungiyar, kuma yake neman kafa tarihin zama mai koyarwa na farko da ya lashe gasar sau hudu a jere a tarihi.
Har ila yau, kungiyar tana ci gaba da fafatawa a gasar ta zakarun Turai inda a ranar Talatar data gabata ta kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a filin wasa na Santiago Barnebue a zagayen kusa da na kusa dana karshe.
Tabbas kungiyar kwallon kafa ta Manchester City tana daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya a yanzu kuma idon kungiyar daya yana kan wasan da za su fafata da Real Madrid a wasa na biyu da za su kece raini a filin wasa na Ettihad da ke Birnin Manchester.
Ragowar wasannin da suka ragewa Manchester City:
Afrilu 13: Luton (H) Afrilu 25: Brighton (A) April 28: Nottingham Forest (A) May 4: Wolbes (H) Mayu 11: Fulham (A) Mayu 19: West Ham (H) TBC: Tottenham (A)
Wasannin da za su ba wa kungiyar Manchester City wahala su ne wasa da kungiyoyin Brighton a gidan Brighton din sai wasa da West Ham da kuma kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a filin wasa na White Hate Lane dake Birnin Landan.
Idan har Manchester City ta iya samun nasara a wadannan manyan wasannin tabbas za a iya cewa zata lashe gasar Firimiya saboda a cikin kungiyoyin guda uku da suke rige-rigen lashe gasar ta bana, Manchester City ce kawai wasanninta ba su da wahala sosai idan aka hada da na kungiyoyin Arsenal da Liberpool masu maki 71 kowacce kungiya.