Manoman Masara a Nijeriya suna gab da farfadowa daga irin asarar da suke tafkawa sakamakon barnar da kwari da kuma karancin ruwa da suke fuskanta a duk shekara, an kiyarsata asarar da ke yi ya kai na fiye da Naira Biliyan 9, wannan na faruwa ne sakamakon sabin irin masara na ‘Tela Maize’ da Cibiyar Binciken Harkokin Noma (IAR) da ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta samar ana kuma gab da fara gabatar dashi Manoman kasar nan.
A kasar da ke da mutane fiye da Miliyan 200 ana kuma samar da Tan Miliyan 12 na masara maimakon Tan Miliyan 18 na masara da ke bukata, a kan haka ake shigo da ragowa Tan miliyan 6 don cike gibin da ake bukata domin amfani a cikin gida.
Baya ga dogaro da shigo da kayan abinci daga kasashen waje matsalolin sauyin yanayi ya sanya ana noma Tan 2.5 zuwa Tan 3 a hecta; tabbas wannan ya yi matukar karanci hakan kuma na daga cikin matsalolin da ke haifar da karancin abinci a wannan lokacin.
A jawabinsa a gonar gwaji na ‘TELA Maize’ da aka yi a karamar hukumar Minjibir ta Jihar Kano a makon jiya, Shugaban Cibiyar Binciken Aikin Noma (IAR) Zariya, Farfesa Mohammad Ishiyaku, ya bayyana cewa, an samar da sabon irin masara na ‘Tela Maize’ ta yadda zai iya jure farmakin kwari da kuma karancin ruwa, a halin yanzu manoma na tsimin fiye da Dala Biliyan 9 (Dala Miliyan 24) a duk shekara wajen magunguna kashe kari da suke saya don yin feshin kadadan fili noma da ya kai hekta 500.
Ya kuma kara da cewa, daga cikin Naira Biliyan 9 da aka kiyasta za a samu manoma za su yi tsimin Naira Biliyan 3 da ake kashewa wajen feshin kadada 500 za kuma a yi tsimin fiye da Naira Biliyan 6 na asarar da ke yi sakamakon illar rashin ruwa a duk shekara.
Farfesa Ishiyaku ya bayyana cewa, IAR ta samu gaggaruwa nasara a fannoni da fama tun da aka fara binciken samar da irin ‘TELA Maize’ musamman a kan gonakin gwaji da aka kafa a sassan kasar inda aka fahimci yadda irin ke iya jure wa fari da farmakin kwari. Ya ce, wadannan nasarorin za su taimaka wajen warware matsalolin da manoma ke fuskanta tare da bunkasa tattalin arzikin kasa wanda zai kai Nijeriya ga dogaro da kai a wajen samar da abinci ga ‘yan kasa.
Ya kuma bayyana cewa, a tsawon shekara 100 da kafa Cibiyar Binciken Harkokin Noma (IAR) na Samaru ta gudabar da bincike da dama a kan kayyakin noma daban-daban wadanda suka kai ga kara yabanyar da manoma ke samu da kuma bunkasa tattalin arzikinsu gaba daya.
A nashi jawabin, shugaban kwamitin samar da irin ‘TELA Maize’ a Nijeriya, Farfesa Rabiu Adamu, ya ce,an fara bincike don samar da irin a Nijeriya ne tun a shekarar 2019 an kuma yi haka ne saboda matsalolin da kwarin ‘Fall armyworm’ da ‘Stem-borers’ ke haifarwa a kan masara wanda hakan ke janyo asarar fiye kashi 80 na masarar da ake nomawa a fadin kasar nan.
Farfesa Rabiu Adamu wanda masani ne a bangaren kwari da yadda suke barnata shuka, ‘Entomology’, ya ce, samar da irin ‘TELA Maize’, zai taimaka wajen rage yadda manoma ke amfani da magunguna kashe kwari wanda hakan zai takaita yadda amfanin dasu ke cutar da muhalli da rayuwar al’umma. Ya ce, samar da ‘Tela Maize aiki ne na wata hadaka data hada da Gidauniyar Inganta Aikin Gona ta Afrika (AATF) a kasasshen Afrika 7 wanda suka hada da Kenya, Uganda, Tanzania, Ethiopia, Mozambikue, Nijeriya da kuma Afrika ta Kudu.
Manoman sun yi maraba tare da nuna jin dadinsu a kan samar da ‘Tela Maize’ wanda suka ce, tabbass zai bunkasa harkar noma a Nijeriya.