Bishiyar dogon-yaro na fara fitar da ‘ya’ya ne daga shekaru uku zuwa biyar, inda kuma take kammala girmanta a cikin shekaru goma.
A duk shekara bihiyar na samar da ya’ya’ da suka kai nauyin kilogiram 50, haka bishiyar na shafe dimbin shekaru a duniya.
Tsawon Wanne Lokaci Irin Dogon-yaro Ke Gama Yin Girma?
Irin na dogon-yaro na da gajeriyar rayuwa, domin yana kai wa daga kwana 10 ne zuwa 12 a lokacin da yake danye, saboda haka, ana son ka tabbatar da ka samu ingantaccen irin da zai yi saurin nuna bayan ka shka shi.
Ana son ka tabbatar da rufe shi a cikin tukunya don ya kasasance yana samun lema, yana kai wa mako uku ne in an shuka shi.
Wace Kasa Aka Fi Samun Bishiyar Dogon-yaro?
A bisa rahotannin masana kan kimiyya da fasaha da kuma binciken da Cibiyar bunkasa aikin noma ta kasa da kasa suka gudanar a shekara ta 1992 sun ce, an fi shuka bishiyar dogon-yaro a Asiya da nahiyar Afirka da kuma wasu kasahen a duniya.
Kusan kashi 60 a cikin dari na al’ummar da ke kasar Indiya na shuka dogon-yaro.
Wace Irin Kasa Dogon-yaro Ya Fi Bukata ?
Dogon-yaro ya fi bukatar kasa mai inganci kuma ba a son ka shuka irin a inda ruwa ya fi yawan zama.
Bangare Bishiyar Dogon-yogo Da Ake Yin Magunguna Da Shi.
Baya ga bihiyar ta dogon-yaro, ana kuma yin amfani da ganyenta da irinta da kuma jikinta wajen yin magungunan gargajiya.
Ya Ya Ake Adana Ganyen Bishiyar Dogon-yaro Ya Dade?
Matakin farko ana son ka cire ganyensa daga jikin bishiyar da ka ciro shi,
Matali na biyu, ana son ka saka Ganyen a cikin wani Kwano sanan ka rufe shi don ya tsotse lemar da ka jikinsa sannan ka rufe shi.
Mataki na uku, saka shi a cikin na’ura mai sanyi.
Yadda Ake Tatsar Man Bishiya Daga Ganyensa
Ana son ka nika shi sannan ka dora shi a kan wuta ka tafasa shi har zuwa mintuna 15 bayan ka sauke shi daga wutar sai ka bar shi ya yi kamar awa biyu ko kuma sama da haka.
Daga nan, sai ka adana shi a gurin da yake busasshe kuma a tabbatar cewa, rana ba ta kai wa inda yake.
Ana Samun Kudi A Noman Bishiyar Dogon-yaro.
A yanzu haka, bishiyar dogon-yaro na kara samun karbuwa a fadin duniya, musamman ganin yadda fannin ke samar da kudaden shiga haka akwai masa’antu da suke sayensa domin sarrfaa shi zuwa wasu nau’uka kamar su, yin magani, man shafa da sauransu.
Bishiyar dogon-yaro na jure wa fari kuma bishiyar ta fi son ma’unin yanayin da ya kai 21°C zuwa 32°C ko kuma 70°F 90°F.
Wani kwararre a fannin na noman Bishiyar dogon-yaro Dakta Abdullahi Ahmed Yar’adua, of neem ya ce, lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali wajen bunkasa noman Dogon Yaro fiye da yadda kasar Indiya ke yi
Dr Yar’adua ya tabbatar da cewa, Indiya na da kimanin Bishiyar Dogon Yaro da suka kai miliyan 20, inda ya kara da cewa, daga shekarar 1985 zuwa 1995, gwamnatin kasar na samun kudaden shiga da suka kai kimanin dala biliyan 2.5 daga man da take samu daga Bishiyar dogon-yaro.
Ya sanar da cewa, ana sarrafa Ganyen wajen sarrafa takin zamani, inda ya dora laifin yadda fanin ke samun koma baya kan yadda shugabain kasar nan ba sa mayar da hankali kan noman Dogon Yaro.
Ya kuma koka kan yadda aka yi watsi da masa’anta noman dogon-yaro da tsohuwar gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ya kafa a jihar Katsina.
Dakta Yar’adua ya kuma shawarci gwamnati da ta mayar da hankali wajen noman Bishiyar Dogon Yaro ganin yadda ake samun kudaden shiga masu yawa.