Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Aisha Saji ta shiga tsakani kan wasu yara masu kankantar shekaru da ake zargin abokin mahaifinsu ya yi lalata da su domin tabbatar da adalci ga wadanda lamarin ya shafa.
Wata sanarwa da Daraktar Wayar da Kan Jama’a ta Ma’aikatar, Aishatu Haruna, wacce ta ba wa LEADERSHIP kwafinta, ta bayyana cewa kwamishiniyar ta dauki nauyin lamarin ne jim kadan bayan an yada labarin a wani shirin gidan rediyon ‘Yanchi da Rayuwa’.
- An Samu Sabuwar Damar Kyautata Hulda Tsakanin Sin Da Hungary
- Mukalar Shugaba Xi: Hakika Kasar Sin Ba Ta Yi Wa Duniya Rowar Kaifin Basirarta Ba
Nan take Kwamishiniyar ta umurci daraktoci biyu da kwararrun ma’aikata da su tuntubi wadanda abin ya shafa tare da ba ta ra’ayi.
A cewar sanarwar, yayin ganawa da daya daga cikin wadanda abin ya shafa da mahaifiyarsa a ofishinta, kwamishiniyar ta nuna kaduwarta matuka da jin irin wannan mummunan aiki da aka aikata ga yaro dan shekara takwas da ya kai ga lalata masa dubura.
Bisa la’akari da halin da mutanen da lamarin ya shafa suka shiga, Saji ta yi alkawarin bin diddigin lamarin har zuwa karshe, sannan kuma ya yi kokarin ganin an samar da wata kafa ta gwamnati da za ta samu nasara a shari’a.
Ta kuma yi tayin biyan basussukan da aka tara na tsawon watanni ana jinyar wadanda abin ya shafa, wadanda har yanzu ba su samu cikakkiyar lafiya daga raunukan da suka samu na dubura ba, sannan ta kara tallafa wa dangin da kyautar tufafi da kudi da buhun shinkafa da masara.
Da take magana tun da farko, mahaifiyar wadanda lamarin ya shafa ta ce tsohon mijinta ne ya sanar da ita lamarin inda ya janye karar kuma ya lallashe ta da ta bar batun kai karar, amma ta yanke shawarar sake bude maganar shari’ar ta hanyar ‘yansanda, sannan ta kai kotu. An bayar da belin wadda ake zargin duk da hujjojin da likitan da ya bayar game da ‘ya’yanta.
Ta kuma kara da cewa, a wata ziyarar jinya, wani likita ya fitar da tsutsotsi da suka taru a duburarsu, ya yi wa yaran dinki a duburarsu lamarin da ya sanya shi zubar da hawaye yayin da dayan da abin ya shafa ya rika gudawa babu kakkautawa.
Sai dai mahaifiyar ta ce, duk da cewa an shigar da karar a gaban kotu, amma har yanzu ba a kira su gaban alkali ba.
A nasu jawabansu na daban, wadanda abin ya shafa ‘yan shekaru takwas zuwa goma sun ce wadanda ake zargin sun yi lalata da su ne ta hanyar yi musu barazanar cutar da su idan sun gaya wa wani irin cin zarafin da aka yi musu.
Sai dai sun bayyana cewa duk da wannan barazanar sun kai rahoton lamarin ga mahaifin nasu wanda ya bukaci su yi shiru tare da gargadar su da su boye maganar.