Fargaba da damuwa na kara karuwa, sakamakon rade-radin da ake yi na shigo da Shinkafa daga Kasar Thailand zuwa Nijeriya, don sayar da ita; wadda ake zargin ta jima a ajiye har tsawon shekara goma ba tare da an yi amfani da ita.
Wannan fargabar dai, ta biyo bayan wata sanawar ce; wadda Gwamnatin Kasar Thailand ta sanar cewa, za ta tura wannan Shinkafar zuwa Kasashen Nahiyar Afirkar; domin sayarwa.
Gwamnatin kasar na shirin yin gwanjon buhunhunan Shinkafar ne guda 150,000, wadda ta ajiye su a runbunanta na ajiya, har tsawon shekaru goma.
Haka zalika, kasar ta Thailand na sa ran sama wa da kanta kudin shiga ne ta hanayr sayar da wannan Shinkafa, domin kuwa yawan kudin ya kai kimamin daga Baht miliyan 200 zuwa 400 na kudin kasar, inda kudin ya kai Dala miliyan 5.4 zuwa 10.8.
Tun bayan da gwamnatin ta Thailand ta bayyana wannan shiri nata ne, wasu masana da wasu ‘yan Nijeriya a shafukan sada zumunta na zamani, suka fara yin mummunar suka a kan wannan shirin na gwamnatin Thailand na turo da wadannan buhunhunan Shinkafar zuwa Nijeriya.
Sun yi sukar ne, duba da yadda yin amfani da Shinkafar zai shafi kiwon lafiyar al’ummar wannan kasa; idan har aka shigo da ita Nijeriya, musamman ganin yadda ba a dauki wasu kwararan matakan da ke sanyo ido a kan ingancin kayan da ake shigowa da su cikin kasar ba.
Wani dan Nijeriya mai suna NwaOnyekuzi, ya wallafa nasa bacin ran a kafarsa ta Di (Tweeter), inda ya ce; wannan shiri na gwamnatin Thailand, cin mutuci ne ga ita kanta Nijeriya.
Bugu da kari, wata kididdiga ta nuwa cewa; daga kakar 2023 zuwa 2024, Kasar Thailand ta kasance ta biyu da ke a kan gaba a fadin duniya wajen safarar Shinkafar da ta kai tan miliyan 8.2.
Wani kwararre a fannin samar da ingantaccen abinci, mai suna James Marsh ya sanar da cewa, wannan Shinkafa wadda ta shafe shekaru goma a ajiye a cikin rumbunan Thailand, sakamakon dadewar da ta yi babu wani sinadari mai gina jikin Dan’adam da za a mora daga cikinta.
A cewarsa, saboda yawan feshen da aka yi mata don kare ta daga lalacewa, zai iya shafar kiwon lafiyar duk wanda ya yi amfani da ita.
Haka zalika, ya yi nuni da cewa, a ka’ida ba a son buhunhunan Shinkafar da aka adana cikin rumbu su wuce tsawon shekaru biyar a ajiye.
Sannan, ya nuna takaicinsa kan cewa; wadannan buhunhunan Shinkafar, za su samu hanyar shigowa cikin kasar nan duba da yanayin da iyakokin Nijeriya suka kasance.
Ya kuma shawarci gwamnatin tarayya cikin gaggawa ta dauki matakan da suka dace, domin dakile shigo da wannan Shinkafa cikin wannan kasa, inda ya kara da cewa; wannan babban aiki ne a gaban hukumominmu.
Har ila yau, ya sanar da cewa; wannan Shinkafa na dauke da lamba wadda za a iya saurin gane ta.
Shi ma wani kwarrre a fannin kimiyyar abinci da ke Jami’ar Aikin Noma ta Tarayya, Farfesa Shittu Akinyemi ya sanar da cewa, kula da ingancin abinci ya kasu kashi biyu ne, wato yadda aka lula da shi da kuma irin magungunan feshin da aka zuba wa hatsin don kare shi daga kwari.
A cewarsa, ana iya adana hatsi har zuwa dogon zango, sai dai; mutane na jin tsoro kan yadda aka ajiye kayan abinci har zuwa tsawon lokaci, musamman ma Shinkafa.