Amincewa Batare Da Samun Sauran Bayanai Ba. A tsakiyar birnin San Francisco ta kasar Amurka, kusa da kwarin silikon (Silicon Balley), akwai wani gida mai lamba 324 yana tsaye a kan titin Jackson. Wannan gida mai murabba’in fiye da kafa 4,000 yana cikin yankin gundumar masu wadata da ake kira da ‘Presidio Heights’. Wannan ginin, wanda a yanzu za a sake masa fasali kuma a mayar da shi a matsayin Cibiyar Musanya Fasahar Dijital ta Nijeriya wadda ake kira a turance ‘Nigeria Startup House’, yana nuni ne da wani muhimmin mataki a yunkurin Nijeriya na samar da sarari a babbar cibiyar fasaha da kere-kere ta duniya.
Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), a taron ta na ranar 13 zuwa 14 ga watan mayu 2024,bisa ga manufofinta mabanbanta na bunkasa tattalin arzikin kasa, ta hanyar jawo hannun jari kai tsaye daga ketare (FDI ), da kuma inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci da aka amince da su kwanan nan, ta zartar da cewa wannan gida zai zama fadan bunkasa fasahar dijital ta Nijeriya a kasar Amurka, toh ýan kasa na fatan, wannan zartarwa da gaske ne kuma zai kawo sauyi mai alfanu da nufin hadaka fasahar dijital (zamani) ta Nijeriya.
- Dimbin Ma’adinan Kasar Nan Sun Isa Su Kore Mana Talauci -Minista
- Sin: Za A Zurfafa Dangantakar Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da Kenya
Wannan babbar kaddara, a tarihi, ta kasance matattarar diflomasiyyar al’adu da ayyukan gudanarwa da ke dauke da karamin ofishin jakadancin Nijeriya.Wannan gida an yi watsi da shi tun bayan rufe shi a shekarar 1989. Kuma an shelanta wa ýan Nijeriya cewa darajarta ta kusan dala miliyan 7. Toh tun da shela ce, akwai bukatar samun ofishin da ake kira ‘Assessor-Recorder’s Ofis ta San Francisco’ don ta samar da kima na kwararru idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu da kuma yanayin kasuwa ,don ka da a yi wa Nijeriya sakiyar da ba ruwa!
Sakamakon Kamuwa Da Cutar Beraye Da Ýan Kama Wuri Zauna
Bisa ga imani, matakin da gwamnati ta dauka na mayar da wannan kaddara mai kima zuwa cibiyar fasaha ba yaudara ba ce ko kuma saboda wasu dalilai na doye, sai dai wata dabara ce ta canza amfani da ita, da kuma amfani da ita wajen samun albarkatun da ke cikin yankin Bay da kuma sanya Nijeriya a matsayi babba da kuma haskaka ta a mtsayin mai taka rawa a fagen fasahar duniya ? Toh ya zama wajibi a yayin da ake wanna gyare-gyaren a dau mataki na jan hankali, gargadi da hanawa, sannan kuma yana da mahimmanci a binciki duk wani sakaci, rashin kulawa da zakulo duk masu hannu da alhakin kyale ta ta fada cikin lalacewa tun daga 1989 zuwa yau kusan shekaru 35 ke nan!
Tambaya – Shin a cikin wannan shekaru akwai rabon kasafin kudi da aka ware domin kulawa da wannan kaddarar? Idan akwai, to ya kamata masu binciken kudi na gwamnatin taraya da kuma binciken almubazzaranci na kudi da kuma hukumar da ke kula da kaddarorin al’umma, su waiwayi wannan al’amari da idon basira kuma a dauki matakan da suka dace a kan wadanda aka samu da laifi, kamar yadda doka ta tanada.
Dabarun Backend da Kuma Frontend
Abin da ‘yan Nijeriya suka sani ya zuwa yanzu su ne: Gwamnatin tarayyar Nijeriya za ta ci gaba da mallakar wanna kaddarar, wanda ma’aikatar sadarwa ta tarayya, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital da ma’aikatar harkokin wajen tarayya za su kula da ita.
Gamayyar kamfanonin fasahar dijital ta Nijeriya ne za su gudanar da wannan cibiya, wadanda za su samar da kudaden da ba na gwamnati ba don gudanar da ayyukan gidan fasaha (Nigeria Startup House).
Shigar da Kwamitin Hadin Kan Tattalin Arziki na Shugaban kasa (PECC), wanda ya hada da sanannun kanfanonin hada-hadar fasaha mai alaka da ma’aikatan gwamnati. Waannan kanfanoni na da kusan kashi 10% na wakilan wanna kwamiti.
Abin da ‘yan Nijeriya ba su sani ba ya zuwa yanzu: Ina alaka ko hadin kai tsakanin Cibiyar Fasaha ta Artificial Intelligence da Robotics (NCAIR) da Cibiyar Musanya Fasahar Dijital ta Nijeriya (Nigerian Startup House)? Shin akwai ma’auni don samo wadannan kamfanoni da su ci gajiyar wannan albarkatun kwarin silikon (Silicon Balley)? Shin yana yiwuwa ga manyan kamfanoni masu neman hadaka harkar su, su amfana da wanna fa’ida?
Sannan, shin asusun bai daya na gwamnatin tarraya (Consolidate Rebenue Fund – CRF) zai amfana daga wannan almari kowace shekara? Shin kofa a bude take ga kanfanoni masu sha’awar shiga wannan kungiyar da za ta kula da wannan Nigeria Startup House? Mene ne tasirin makudan kudi na dala biliyan 1.3 da wannan kanfanoni suka samu a cikin shekarar bara 2023 ta hanyar hannun jari ga asusun bai daya na Nijeriya (CRF) ta fuskar haraji da makamantan su? Jerin tambayoyin suna nan ba iyaka!
Alamu sun nuna cewa al’amarin a lullube da kuma cikin siri ake yin sa, amma amsoshin suna da mahimmanci, saboda za su ba da hanyar fahimtar inda Nijeriya ta dosa idan aka yi la’akari da mahimmanci da darajar wannan kaddara da kuma kasancewar yiwuwar son kai da za a iya fuskanta.
Yana da matukar muhimmanci a tabbatar da cewa aikin gudanarwan ya bi ka’idojin kwantaragin Nijeriya na shekarar 2007 (wato Public Procurement Act 2007) da kuma ka’idojin da’a ga jami’an gwamnati ( wato Code of Conduct for Public Officers ) domin yana da matukar muhimmanci a guji duk wani abu da ya saka wa ka’ida tare da tabbatar da cewa jami’an gwamnati ba za su yi amfani da mukamansu don amfanin kansu ba!
Batun Application Programming Interfaces (APIs) da Gateways: Kamar yadda Ma’aikatar sadarwa ta tarayya, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital ke daukar wannan mataki mai santsi, akwai bukatar gabatar da Dokokin Gudanarwa (wato Hanyoyi da Kofofi), kuma ya kamata a yi shi tare da wayar da kan jama’a game da ma’anar wannan shirin da tasirin, da kuma bisa bin tsarin shari’a da da’a masu dacewa wadanda ke tafiyar da irin wadannan ayyukan. Kamar yadda yake da matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasara da kuma tabbatar da alfanun da aka yi niyya ga tattalin arzikin Nijeriya da matsayinta a fagen kasa da kasa
Kila ka’idodin da za su jagoranci dokokin gudanawar su kunshi: Dokar Jariran Kamfanonin Nijeriya 2022 (wato Nigeria Startup Act 2022) – Ko da yake har yanzu ba a auna tasirin dokar ba saboda tana kan matakinta na kuruciya. Don haka, yiwuwar yin karo da juna tsakanin Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta kasa (NITDA) da Majalisar kirkirar Dijital da Kasuwanci (NCDIE) za su zama kalubale. Lakabin Jaririn Kanfani da kuma lokacin da kanfanin zai canza zuwa lakabi na balagagen kamfani.
Sai kwantaragin Nijeriya na shekarar 2007 (wato Public Procurement Act 2007) – Yana da kyau su kai ziyara; Sashe na – 24 zuwa 49, Sashe na – 50 zuwa 59, Sashe na – 62 zuwa 63 da kuma Sashe na – 64, da dai sauransu.
Yarjejeniyar kasa da kasa da sauran yarjejeniyoyi masu alaka da wannan fannin
Wannan Ababe Turanci Ne Kai Sosai
Akwai sifofi guda biyu masu alaka da juna da ya shafi wannan fanni ta fasahar dijital:
Na farko, Sharuddan Kwamiti (wato Terms of Reference) na PECC sun hada da tsarawa da aiwatar da ingantaccen tsarin tattalin arziki na gaggawa, magance kalubalen tattalin arziki nan take, da tabbatar da ingantaccen aiwatar da dabarun tattalin arziki. Majalisar ta umurci kwamitin da ta gabatar da wani cikakken tsari da zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki a shekarar 2024 cikin watanni shida masu zuwa.
Na biyu, an tsara da kuma fitar da muhimman abubuwan da suka shafi ciniki da kirkire-kirkire, kasuwanci da jari-hujja (IEC). Wannan Dabarun Tsare-tsare (wato Strategic Blueprint Pillars) an tsara su ne don hadaka sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya da hadaka ta ta hanyar fasahar kere-kere. Shi tsarin Kuma yana da ginshikai guda biyar, kamar haka; Ilimi (Knowledge), Tsrae-tsare (Policy), Kayan aiki (Infrastructure), Kirkire-kirkire, Kasuwanci da hannun Jari (wato Innobation, Entrepreneurship & Capital-IEC) da kuma Cinikayya (Trade).
Wadannan su ne ‘gobbledygook’ in ji Bature, muna cikin karni ne wanda fasahar dijital ke jagoranta, tare da yara masu hazaka wajen yaudara ta hanyar fasahar dijital (wato yahoo-yahoo boys & girls), tun ba su balaga ba sun shiga hanun EFCC tare da wasu suna tsare kuma da yin wa’adi daban-daban a gidajen Gyara Halinka (wato Correctional Institutions), wane shiri ko tsari aka yi masu a can da kuma lokacin da suka fito ko kuma wadanda ke yawo yanzu haka a kan tituna?
Wadancan ginshikan na sama ba su da wani alamar tasiri da zai samar da tushen dabarun da Nijeriya ke bukata da kuma yin amfani da su don samun karfin canza akalan Nijeriya ta hanyar fasahar dijital da kirkirai-kirkirai, harma asa ran zasu taimaka sukai Nijeriya tudun mun tsira ko da da tsalen imani ne kuwa!
Filin Wasan Masu Hanu da Shuni (Millionaires Play Ground)
Samun damar kafuwa a Silikon Balley na kasar Amurka na cike da kalubale wadda take bukatar dabaru da kuma sanin zamantakewa domin ba wajene na halayen cin amanar kasa ba.
Wanna yanki na Bay Area, shi ne tushen fasahar dijital a duniya kuma akwai sama da kanfanoni 200 manya – manya da suke da kudaden shiga mai darajar sama da dala biliyan 900. To lalle kam wannan waje yana da tagomashi da lagwada kuma abin farin ciki idan da zai iya taimakawa ya zamo silar fitowar Nijeriya daga cikin hallin tabarbarewan tatalin arziki.
Fatan ’yan Nijeriya a nan shi ne alkawarin samun hannun jari ga kamfanonin Nijeriya da ke cikin harkan fasahar dijital zai tamaka kwarai wajen samun karin kudaden shiga da kuma guraben samun aiki. Toh amma wannan shine hakikanin gaskiyar maganar?