Da farko ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.
Mai karatu wannan fili na ciniki da kasuwanci na fara yin sa a wannan jaridar mai albarka tun shekarar 2008 zuwa 2010. Tun daga wancan lokacin wato shekarar 2010 na tafi hutu ko kuma shi shafin nawa ya tafi hutu sai yanzu a cikin ikon Allah ya sake dawo da ni domin ci gaba da wannan babban muhimmin aiki ko na ce rubutu.
A wancan lokacin na yi tsokaci da bayanai ta yadda ya kamata dan kasuwa mai karamin karfi da mai babban karfi ya yi don samun ribar kasuwancin da ya ke yi ko take yi ko ku ke yi.
Alhamdullah na samu wasiku da kiraye kirayen waya tun wancan lokacin daga ‘yan kasuwa da yawan gaske domin godiya da karin bayanai a bisa abubuwan da na yi batu a kansu. Jaridar LEADERSHIP HAUSA hakika ta ciri tuta saboda damar da suka bani na wayar da kan jama’a afannin kasuwanci da cinikayya daban-daban, hakan ta sa da yawa jama’a kasuwancinsu ya ci gaba ta inda ba’a zato.
Kuma saboda samun bayanai da ga wurin mutanen da suka amfana da rubutun da na sha yi a kan batutwa daban-daban su ne suka sa ni na ga dacewar na kara dawowa don ci gaba da aikin ta yadda za’a kuma taimakawa sabbi da tsofaffin ‘yan kasuwa gudanar da sana’oinsu.
Har’ila yau yanzu mun shiga wani sabon juyi da ita kanta kasuwa ko in ce shi kansa kasuwanci ya dauki sabon salo saboda abubuwa da yawa da suka faru da kuma suke ci gaba da faruwa a duniya ta fannin tattalin arziki.
A wannan mako zan fara ne da bayani akan alfanun kananan sana’oi da yadda suke kawo ci gaba ga jama’a da gwamnati. Wakakil mai karatu idan aka ce kananan sana’oi abin da zai fara zuwa kwakwalwarsa shi ne sana’oi; ‘yan kanana da ake yi da kudi ‘yan kadan, wasu kuma abin ba haka zai zo musu ba zai zo musu ne ta sana’oi da ake yi a gidaje ko ‘yan shaguna irin na cikin unguwanni da cikin kasuwanni.
To koma menene ya zo a kwakwalwarka mai karatu zan yi maka bayani menene kananan sana’oi, saboda haka zaka iya fahimta kuma ka dora sana’arka a cikin rukunin kanana ko manyan sana’oi.
Menene Kananan Sana’oi? Ma’anar kananan sana’oi ya danganta da wace kasa ce ko a wace nahiya wannan sana’oin suke. Misali a kasar Amurka kananan sana’oi su ne sana’oin da mutum yake kafawainda ya ke daukar ma’aikata daga mutum 10 zuwa 50.
To abin kula a nan shi ne, mu irin wannan sana’ar sai muce sai kamfani, domin kuwa akwai karamar masana’antar da take da mutane 50 ko kasa da haka, amma sai a rika ganin wannan sana’ar babbar sana’a ko kuma kamfani.
Amma idan mu ka zo nan Nijeriya inda muke, sai mu duba mu ga mecece karamar sana’a ko kananan sana’oi?
Ma’aikatar Kasuwanci ta Kasa, ta raba kananan sana’oi gida uku. Na farko su ne ‘yan-kananan sana’oi wadanda da turanci ake kiransu da ‘’micro small enterprises’’ wannan rukuni na ‘yan-kananan sana’oi ya kunshi sana’ar da mutum ya kafa kuma yake da mutane daga mutum daya zuwa tara a matsayin ma’aikatansa.
Sannan wadannan irin sana’oi kamar wuraren sayar da abinci a gefen manyan tituna za’a iya saka su a cikin wannan rukuni, da kuma sauran sana’oi birjik da ake yinsu wadanda suke daukar mutane tara a matsayin ma’aikata.
Har ila yau, sana’oi da mutane suke yi musamman mata a cikin gidajensu suma sun fada cikin wannan rukunin. Kai bugu da kari hatta masu sayar da kayayyaki a gefen titi wadanda su kadai ne suke gudanar da sana’ar kamar masu sayar da rake, da yalo da mangwaro da lemo da ayaba. Hada da mata masu soya kosai da awara da masu sayar da wake da shinkafa, da mai sayar da naman balangu, da mai sayar da kayan gwanjo a titi, ko a tafe da sauransu, duk sun fada cikn wannan rukunin kananan sana’oi.
Sai rukuni na biyu su ne; Kananan sana’oi wadanda sun dara na farko. Su kuma suna daukar ma’aikata daga mutum 10 zuwa 49. Suma wadanan sana’oi muna nan da su birjik a kasarnan kamar manyan kantunan sayar da kayayyakin masarufi a gurare fitattu a cikin garuruwan Nijeria, da gidajen sayar da burodi da wuraren gyaran motoci da babura.
Abin da ya sa nasa wuraren gyaran motoci da babura shi ne, suma wadannan mutanen masu sana’a ne amma ba ta kasa kaya a kanti ko titi ba, a’a su suna bayar da fasahar da suke da ita ne ga mutane masu matsalar irin abin da suke bayarwa. Misali mai gyaran mota yana ba yar da wani abu ne wai shi ‘serbice’ wato aiki a matsayin abin da yake sayarwa.
Saboda haka shi ma mai sana’ar hannu dan kasuwa ne amma ba mai sayar da kayan da ake gani ba, shi yana sayar da aiki ne wato wata fasaha da yake da ita yake sayarwa ga mutanen da suke da wata matasala wacce shi ne ya ke da maganinta. Kamar dai mai gyaran mota ko babur ko keke da sauransu.
Rukuni na uku sune; Matsakaitan sana’oi wadanda da turanci ake kiransu ‘medium small enterprises’ su kuma wadannan sana’oi suna bayar da aiki ga mutane da suka kama daga 50 zuwa 249, tirkashi mai karatu duk sana’ar da za ta dauki mutum har sama da dari biyu aiki ai wannan sai babban kamfani.
To amma da yake komai na duniya akawai tsari duk kamfanin da yake da mutanen da ba su wuce 249 ba a matsayin ma’aikata wannan kamfanin a idon gwamnati da masana kasuwanci matsakaicin kamfani ne ko kuma na ce matsakaiciyar sana’a ce. Watakil kaima da kake karanta wannan bayanin wasu kamfanonin sun zo maka a ranka, a matsayin matsakaitan sana’oi saboda yawan mutanen da suka ba wa aiki.
Hakika kananan sana’oi su ne kashin bayan duk wani ci gaban tattalin arzikin kasa. A Nijeriya a wata kididdiga ga ma’aikatar kasuwanci ta gwamnatin tarayya ta yi ta nuna cewa akwai kananan sana’o’i a Nijeriya guda miliyan talatin da bakwai da dubu dari bakwai (37,700,000) wannan kididdiga ta nuna cewa kashi tamanin da hudu na ayyukan yi a Nijeriya suna cikin waddannan sana’oi daban-daban wato idan aka lura kenan, aikin da sana’oi suke ba wa ‘yan Nijeriya ya doke wanda gwamnatoci suke bayarwa.
Sannan har ila yau kididdigar ta nuna cewa jihohi guda uku a Nijeriya sun fi yawan wadannan kananan sana’oi rukuni uku, jihohin su ne Legas da Oyo da Kano. Sannan kuma kididdigar ta nuna wadannan sana’oi su ne kashin bayan juya tattalin arzikin Nijeriya domin kuma sune suke ba wa ‘yan Nijeriya aikin yi fiye da gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da gwamnatocin kananan hukumomi.
Abin tambaya shi ne shin wadannan sana’o’i’n kwalliya na biyan kudin sabulu kuwa ga masu yinsu?
Sannan gwamnatcinmu suna taimkawa irin wadannan sana’oi a matsayinsu na masu taimaka wa tattalin arzikin Nijeria?
Zamu ci gaba a mako mai zuwa