Gabatarwa:
A jerin littattafan Adabin Zamani/Rubutaccen Adabi da Hukumar shirya jarabawa ta matakin iya karatu da rubutu don kananan Makarantun Sakandare ta fitar, don shekarar 2017 zuwa 2019 don dalibai da Hausar ce harshensu na uwa ko na farko (list of literature set books for Basic Education Certificate Edamination 2017 – 2019 Hausa L1), akwai:
ZUBE
1. Sidi Ya Shiga Makaranta na Umaru Ladan da Michael Crowder da kamfanin dab’i na Jami’o’in Afirka da ke Ibadan ya wallafa a shekarar 1981.
2. Tauraruwa Mai Wutsiya na Umaru Dembo da Kamfanin dab’i na Arewa wato Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1969.
- Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Allah Ya Fi Son Kyawawan Ayyukan Da Aka Yi A Kwanakin
- Falalar Goman Farko Na Watan Fahimtar Sayyidina Umar (RA) Da Sayyidina Aliyu (RA) Kan Ramakon Ramadan A Goman Zulhajji
WASAN KWAIKWAYO
1. Zaman Duniya Iyawa ne na Yusuf Ladan da kamfanin dab’i na Arewa (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 2004.
2. Malam Mahamman na Muhammad Bello da kamfanin dab’i na Arewa na (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1981.
WAKA
1. Wakokin Hausa na Suleman Na’ibi Wali da sauransu da Kamfanin dab’i na NNPC da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1982.
To da yake ni aka dankawa ‘yan aji daya na karamar Sakandare (JSS1) don koya musa wadannan littattafai, sai na yanke shawarar mu soma da karanta littafi na farko na zube wato Sidi Ya Shiga Makaranta.
Mun soma karanta littafin a aji tare da dalibai sai dai kamar yadda na ci karo da kurakurai a littafin wasan kwaikwayo na Kulba Na |arna na Umaru Danjuma, a shekarar bara lokacin da nake koyar da ‘yan aji daya na babbar Sakandare (SS1), har Jaridar Leadership ta Hausa ta dau mako biyu tana bugawa (28/3/2013 zuwa 4/4/2014), haka nan muka ci karo da irin wadannan kurakurai a littafin Sidi Ya Shiga Makaranta.
Kurakuran da suke cikin Sidi ya shiga Makaranta.
Littafin zube na Sidi Ya Shiga Makaranta yana da shafi tamanin da shida (86) da babi tara. Littafi ne dan karami da aka yi masa kirar saukin dauka (Nobel). Mai launin kore da zanen hoton Sidi da suma irin ta ‘yan makaranta a wadancan shekaru a bangon littafin na gaba, da hoton wani da babbar riga da doguwar hula a bayan Sidi, sai kuma ginin soraye irin na gidajen sarauta a can bayansu. Sai bangon baya na littafin inda aka yi bayanin marubutan littafin, da bayanin cewa littafin fassara ce daga littafin Sani Goes To School.
Inda ni ne zan fassara ‘Sani Goes to School’ da zan sa ‘An Sa Sani A Makaranta ko An Kai Sani Makaranta. Tunda dan makarantar Firamare dai sa shi ake yi a makaranta ba shi yake shiga makaranta da kansa ba ballantana a ce Sidi Ya Shiga Makaranta. Amma fa ra’ayina ne.
A kasan sunan littafin an rubuta marubutan wato UMARU LADAN & MICHAEL CROWDER. Gyaran a nan maimakon & da aka sa, da an sa DA. Ya zama UMARU LADAN DA MICHAEL CROWDER.
A babi na daya shafi na daya layin farko an rubuta wani ya doka sallama daga waje. Maimakon Wani ya doka sallama daga waje.
A sakin layi na uku jimlar farko an rubuta ya ji karar mota, maimakon ya ji dirin mota.
A jimla ta gaba an rubuta ba wai santin furar da ya ke sha ne kawai ba, maimakon ba wai santin furar da yake sha ce kawai ba.
Sai sakin layi na hudu inda aka rubuta kugin lanroba, maimakon dirin landiroba.
Can kusa da karshen sakin layi na hudu an rubuta ‘Ganin haka sai Sidi ya hakura da zuwa kallon motar, Ya yi ta shafa fitullun motar gaba da baya. Ya lelleka karkashin motar kamar makaniken da ke neman abin da ya lallace.
Sidi da ya hakura da zuwa ganin mota, sai kuma aka ce yana ta shafa fitullun motar? Sai kalmar MAKANIKE. Tabbas kalma ce ta aro daga Ingilishi MECHANIC. Sai dai BAKANIKE ni dai na ji Bahaushe yana cewa.
A shafi na biyu sakin layi na biyu an rubuta da idai, maimakon daidai.
Sai sakin layi na kusa da na karshe a shafin na biyu da aka rubuta in ji, maimakon In ji.
A shafi na uku sakin layi na farko an rubuta sadad da, maimakon sanar da. A sakin layi na biyu aka rubuta ya yi, maimakon Ya yi.
A sakin layi na uku cikin shafin na uku an rubuta tal kwabonsa, maimakon tal-kwabonsa. An rubuta ya ke, maimakon yake.
A karshen sakin layi na uku an rubuta wani ne, maimakon wane ne?
A shafi na hudu sakin layi na biyu an rubuta dakyau, maimakon da kyau. an rubuta ka ke maimakon kake. An rubuta tafiyad da, maimakon tafiyar da. A dai wannan shafi aka rubuta a ke, maimakon ake.
A sakin layi na uku an rubuta duk kasan nan, maimakon duk kasar nan/kasarnan kodayake akan samu naso a nan. An rubuta sa mun, maimakon samun. An rubuta ciyad da, maimakon ciyar da. An rubuta umurceni, maimakon umurce ni. An rubuta Afril, maimakon Afrilu. An rubuta faduwan ruwan farko, maimakon faduwar ruwan farko. An rubuta in haka ya faru, maimakon in haka ta faru.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa
Is’hak Idris Guibi
Malami a Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha Ta Tarayya da ke Kaduna
[email protected]
08023703754