• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

by Leadership Hausa
1 year ago
Tsaro

An fara gudanar da wani muhimmin taro na masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya a Jihar Zamfara.

Taron, wanda aka fara shi Litinin ɗin nan a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, ofishin kula da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifuffuka na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Nijeriya ne ya shirya shi.

Mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu Litinin ɗin nan a Gusau, ya bayyana cewa taron, wani shiri ne fayyacewa da lalubo hanyoyin mayar da martani game da matsalolin harkar tsaro da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

  • Yajin Aiki Ya Hana Sauraren Shari’ar Sarakunan Kano

 

Sulaiman Bala ya ƙara da cewa, wata tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙarƙashin jagorancin Oliver Stolpe, wanda kuma shi ne wakili a Nijeriya na UNODC, taron zai tattaro masu ruwa da tsaki, inda za su zauna na tsawon kwanaki uku.

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

Sanarwar ta ce, “A wani muhimmin abu na masu ruwa da tsaki, ofishin kula da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifuffuka na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNODC) ya shirya wani taron ƙara wa juna sani na kwana uku a kan harkar tsaro yau a Gusau.

“Taron ya samar da masu ruwa da tsaki na cikin gida, da wasu baƙi daga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda za su yi zuzzurfan nazari, samar da hanyoyin magance duk wani yanayi na tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar Zamfara.

“Taron ya bayyana ingantattun ayyuka da kuma hanyoyin da za a bi daga ciki da wajen Nijeriya wajen tunkarar waɗannan ƙalubale don samar da wani shiri na haɗin gwiwa.”

A jawabinsa na buɗe taron, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, ƙwaƙƙwarar tawaga ta masana daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna aniyarsu ta haɗin gwiwa wajen magance ƙalubalen da ke addabar Zamfara, da suka haɗa da ’yan bindiga da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Ya ce, “Kwanan nan na ziyarci Majalisar Ɗinkin Duniya domin neman shiga tsakani don magance wasu matsalolin da muke fuskanta, inda na samu kyakkyawar alaƙa da Amina J. Mohammed, mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma sauran ɓangarorin da take jagoranta ciki har da shugaban ofishin kula da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.

“Saboda haka, wannan taron ƙara wa juna sani shaida ne na himmar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke da shi na cika alƙawuran da ta ɗauka don taimaka mana mu ƙara fahimtar yadda za mu magance ƙalubalen da mu ke fuskanta. Muna matuƙar godiya.

“Sama da shekaru goma, Zamfara tana fama da waɗannan matsalolin da ke kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar al’ummarmu da kuma kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Don haka gwamnatina ta ɗauki wannan ziyara da taron bita da muhimmanci, domin sakamakon zai nuna yadda manufofinmu za su kasance wajen dabarun yaƙi da waɗannan ƙalubale.

“Na yi farin cikin ganin cewa za a tattauna batutuwa da dama yayin taron.

“Waɗannan sun haɗa da bayyanar da tushen matsalolin rashin tsaro da aikata laifuka a jihar, kamar garkuwa da mutane, satar shanu, haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, da rikicin ƙabilanci, rawar da jami’an tsaro daban-daban na jihohi da cibiyoyin gargajiya suke takawa wajen yaƙar matsalolin, tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ga ƙarfafa shari’a a aikata laifuka.

“Hanyoyi da yanayin da ke haifar wa al’umma shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara da wanda za a bi wajen rigakafin shan muggan ƙwayoyi da sauran muhimman batutuwa, duk an shirya su don tattaunawa a wannan taro.

“Ina kira ga mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar kuma su bada himma don cin gajiyar ayyukan. Ya kamata ku saurara, ku koya, kuma ku bada gudunmawa mai inganci.

“A ƙarshe, ina fatan dukkanin mahalarta taron za su kasance masu amfanar al’umma. Kamar yadda na bayyana, shawarwarin da aka samar a nan za su kasance masu muhimmanci wajen tsara dabarunmu da ayyukanmu don magance matsalolin da mu ke fuskanta.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
Manyan Labarai

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP
Labarai

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
Next Post
Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Na Zanga-zanga Kan Ƙarin Ƙudin Wutar Lantarki A Nijeriya

Yajin Aiki: An Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati Da NLC/TUC, Za A Koma Teburin Sulhu

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.