• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ke Dagula Rashin Tsaron Nijeriya – Babban Hafsan Sojin Sama

by Leadership Hausa
1 year ago
in Manyan Labarai
0
Abin Da Ke Dagula Rashin Tsaron Nijeriya – Babban Hafsan Sojin Sama
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babban hafsan hafsa sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya danganta fafatawar da ake yi a tsakanin kasashen Amurka, Rasha da China a nahiyar Afirka, da kuma janyewar sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, a matsayin lamarin da ya kara ta’azzara kalubalen tsaro a yankin Sahel wanda ya haifar da kwararar makamai da ‘yan ta’adda zuwa Nijeriya.

Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ganawa da hafsoshin reshe da kwamandojin rundunar sojin sama da daraktoci da kuma daukacin manyan jami’an rundunar sojin saman Nijeriya a Abuja.

  • Wakilin Sin Ya Yi Bayani Kan Matsayin Sin Kan Kare Hakkin Dan Adam
  • Sin Na Goyon Bayan Kokarin Kasashen Afrika Na Magance Matsaloli Ta Hanyar Da Suka Zaba

Da yake jawabi a wajen taron wanda ya zo daidai da shekara guda da ya yi a kan karagar mulki, Air Marshal Abubakar ya ce yakin Rasha da Ukraine ya hana NAF samun kayyakin jiragen sama da kuma kula da jirage masu saukar ungulu na Mi-series wadanda ke da matukar muhimmanci a ayyukanta na yaki da ta’addanci.

“Yayin da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro, kasar Amurka ta ba da goyon baya wajen sayen jiragen sama da makamantansu domin yaki da ta’addanci. Hakazalika, sojojin saman Nijeriya sun samu jiragen sama da alburusai daga kasashen China da Rasha kuma suna ci gaba da yin hadin gwiwa a fannin soji. Daidaita wadannan alakoki na da matukar muhimmanci ga muradun tsaron Nijeriya”.

Ya kara da cewa harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba 2023 da kuma hare-haren da ‘yan tawayen Houthi ke kaiwa kan layukan jiragen ruwa ta tekun Bahar Maliya sun kuma yi “mummunan tasiri wajen samun fasahohin zamani da ake yayi kamar jiragen sama marasa matuka, da sadarwar tauraron dan adam da kuma kirkirarriyar basira ta AI.”

Labarai Masu Nasaba

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Ya kuma kara da cewa karuwar juyin mulki da kuma ficewar kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar daga kungiyar ECOWAS na da mummunar tasiri ga tsarin tsaro na yankin bai-daya a tsakanin Nijeriya da kasashen.

Ya yi nuni da cewa, hukumomin sojan kasar sun koma kasar Rasha domin neman taimakon tsaro, sakamakon gazawar kungiyar ECOWAS wajen magance tashe-tashen hankulan masu ikirarin jihadi a kasashen. .

“Bugu da kari, janyewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya daga MINUSMA, da sojojin Chadi 2000 daga Mali, da kuma sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, na iya kara tsananta kalubalen tsaro a yankin Sahel, lamarin da ya haifar da kwararar makamai da ‘yan ta’adda. A ko da yaushe, wannan lamarin yana kawo cikas ga kokarinmu na yaki da ta’addanci.”

Ya yi gargadin cewa, “Saboda haka, da alama za mu shaida karuwar irin barazanar da aka fuskanta a baya. Don haka, ba wani riba ba ne, dole ne mu himmatu tare da kara himma wajen cimma burin gwamnatin Tarayya da ‘yan Nijeriya na samun wani mataki da zai kai mu ga samun nasara.

Sai dai kuma ya bayyana cewa NAF a cikin watanni 12 da suka gabata ta samu gagarumin ci gaba wajen yaki da ta’addanci, da ‘yan fashi, da masu satar mai da sauran ayyukan miyagun laifuka a kasar nan.

“Duk da haka, akwai sauran abubuwa da yawa da za a yi. Halin da ake ciki na matsin tattalin arziki – yawan rashin aikin yi na matasa, karuwar hauhawar farashin kayayyaki da kuma yawan talauci sun kara dagula yanayin tsaro a kasar. Don haka, dole ne mu yi wannan taron don samun nasara duba da yadda muka gudanar da ayyukanmu a cikin watanni 12 da suka gabata wajen kawo sauyi ga rundunar sojin saman Nijeriya domin biyan bukatun tsaron Nijeriya yadda ya kamata,” in ji shi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Air Marshal Hasan AbubakarNijeriyaTsaro
ShareTweetSendShare
Previous Post

Garambawul Da Muke Wa Tsarin Aikin Sojojin Nijeriya –Janar Musa

Next Post

Badaƙalar Bashin Kaduna: Abin Da Ya Sa Ba Mu Gayyaci el-Rufai Ba – Hon. Lawal

Related

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa
Manyan Labarai

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

6 hours ago
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

23 hours ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

1 day ago
An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Manyan Labarai

An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

1 day ago
Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Buƙatu 10 A Gaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano

2 days ago
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

2 days ago
Next Post
Badaƙalar Bashin Kaduna: Abin Da Ya Sa Ba Mu Gayyaci el-Rufai Ba – Hon. Lawal

Badaƙalar Bashin Kaduna: Abin Da Ya Sa Ba Mu Gayyaci el-Rufai Ba - Hon. Lawal

LABARAI MASU NASABA

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

July 27, 2025
Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

July 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

July 27, 2025
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

July 27, 2025
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

July 27, 2025
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.