Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) reshen Sokoto/Zamfara ta yi gwanjon litar man fetur 25,162 ga jama’a a jihar Sokoto.
Shugaban hukumar da ke yankin, Kamal Muhammed ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Sokoto ranar Laraba.
- Ku Shirya Kare Kanku Ga Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa – Majalisar Kaduna
- Dole Ne Mu Kiyaye Martabar Sarkin Musulmi – Malamai
A cewar Muhammed, gwanjon ya yi daidai da wasu dokoki da kuma amincewar Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, Mista Bashir Adeniyi.
Muhammad ya bayyana cewa, bambancin farashin man fetur tsakanin Nijeriya da sauran kasashen yammacin Afirka ya sa ake fasa-kwaurin man domin samun riba ga masu fasakwaurin.
Muhammed ya kara da cewa fasa kwaurin man fetur na ci gaba da haifar da karancinsa a wasu sassan kasar nan.
Ya ce gwanjon ga jama’a an yi ne akan Naira 180 ga kowace lita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp