Shugaba Bola Tinubu ya mika ta’aziyya ta zuciya ga gwamnatin da al’ummar Jamhuriyar Vietnam bayan rasuwar Sakataren Janar Nguyễn Phú Trọng. A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Shugaban kasa, Ajuri Ngelale, Tinubu ya jaddada muhimmancin rawar da Nguyễn Phú Trọng ya taka a matsayin Sakataren Janar na Jam’iyyar Communist ta Vietnam da kuma lokacin da ya yi a matsayin Shugaban kasa daga shekarar 2018 zuwa 2021.
Nguyễn Phú Trọng shi ne shugaban Politburo da kuma Kwamitin tsaro, mukamai da suka ba shi damar yin tasiri sosai wajen bunkasa ci gaban Vietnam da tafiyar da al’amuranta. Tinubu ya bayyana irin gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban kasar, yana mai jaddada irin tasirin jagorancinsa a harkokin siyasar Vietnam.
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
- Tinubu Ya Isa Ghana Don Halartar Taron Kungiyar Tarayyar Afirka
Shugaban Tinubu ya kuma bayyana jimaminsa ga matar marigayin, Madam Ngô Thị Mận. Ya nuna alhini bisa rashin da ta yi, tare da tabbatar wa al’ummar Vietnam cewa Nijeriya na tare da su a wannan lokaci na juyayi, yana mai jaddada dangantaka mai karfi tsakanin kasashen biyu da kuma bakin cikin da suka sha tare bisa rashin wannan babban jagora.