Gwamnatin Tarayya ta gabatar da buƙatar ƙarin Naira tiriliyan ₦6.2t akan kasafin kuɗi na Naira tiriliyan ₦28.7t da aka riga aka gabatar don shekarar 2024. Wannan buƙatar, wadda Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa, Senator Atiku Bagudu, ya bayyana, na nufin tallafawa ayyukan ci gaba irin su hanyoyi, da layin jirgin kasa, da kuma aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na kasa.
Ƙarin kuɗaɗen za su tallafa wa ayyuka muhimmai kamar hanyar Lagos zuwa Calabar, da kuma layin jirgin ƙasa na Fatakwal zuwa Maiduguri.
- Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa
- Kada Ku Cire Tsammani Da Gwamnatin Tinubu – Adam Oshiomole Ga ‘Yan Nijeriya
Bagudu ya bayyana cewa ƙarin kasafin kuɗin ya ƙunshi Naira tiriliyan ₦3.2t don kashe kuɗaɗen a kan ayyukan ci gaba da Naira tiriliyan ₦3t don abubuwan ci gaba da suka shafi mafi ƙarancin albashi. Ya jaddada cewa kuɗaɗen za su magance giɓin da ake da shi a ayyukan ci gaba na kasafin yanzu da kuma bunƙasa ci gaban kasa.
Ministan ya kuma bayyana cewa ƙarin kuɗaɗen za su taimaka wajen shawo kan jinkirin da ake yi a ayyuka muhimmai da tabbatar da kammala manyan ayyukan da aka ƙuduri niyya.