”An fara kada ganga, ana jiran masu taka rawa su hau dandali. ” Wannan shi ne yanayin da na ji a nan kasar Sin, yayin da ake jiran budewar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC.
A kwanakin nan, an yi ayyuka da dama masu alaka da hadin kan Sin da Afirka, wadanda suka hada da wani dandali na karfafa mu’ammalar al’ummar Sin da ta Afirka, da ya gudana a lardin Hunan na Sin, da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin fasahohin zamani na dijital, da aka gudanar a birnin Beijing na Sin.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Sin Ta Gabatar Da Shirye-shiryen Taron Kolin FOCAC Na Shekarar 2024
- Jami’ai Sun Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Karkashin Dandalin FOCAC
Ban da haka, wata tawagar yaran kasashe daban daban dake nahiyar Afirka ta zo kasar Sin bisa gayyatar da aka yi musu, inda yaran suka samu damar samun karin ilimi dangane da al’adun gargajiyar Sin. Haka zalika, an yi tarukan karawa juna sani a wurare daban daban dake Afirka, inda aka tattauna damammakin neman ci gaba da matakan kara zurfafa gyare-gyare na kasar Sin za su haifarwa kasashen Afirka. Daga bisani, a jiya, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da gudanar da taron koli na FOCAC na shekarar 2024 tsakanin ranar 4 zuwa ta 6 ga watan Satumban bana, batun da ya yi kama da buga ganga da karfi, don samar da kara mai sanya mutum zumudi.
Dandalin FOCAC yana daya daga cikin manyan tsare-tsaren hadin gwiwa na duniya, wanda ya shafi hadin gwiwar kasar da tattalin arzikinta ke tasowa mafi girma a duniya, wato kasar Sin, tare da nahiyar da aka fi samun kasashe masu tasowa, wato nahiyar Afirka. Dandali ne mai muhimmanci a duniya, ganin yadda ya shafi burin neman ci gaba na al’ummar da yawansu ya kai biliyan 2.9, duk a kasashe masu tasowa.
A wannan karo, an saka ma taron koli na dandalin FOCAC jigon ”Hada gwiwa don tabbatar da zamanantarwa, da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka dake da matukar inganci”, wanda ya nuna cewa, za a mai da hankali kan hada tsare-tsaren raya kasa na bangarorin Sin da Afirka waje guda, da neman samun karin damammakin hadin gwiwa don amfanin juna, da kokarin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon mataki.
Sai dai wadanne alfanu ne taron kolin FOCAC na wannan karo zai haifarwa kasashen Afirka? Ta la’akari da yanayin gudanar da dandalin FOCAC na mutunta juna, da daidaituwa, da tattaunawa tare, to, za a san cewa, za a lura da bukatun kasashen Afirka a wajen taron da zai gudana, kana za a gamsar da su bisa daidaita moriyar bangarorin Sin da Afirka.
Yanzu haka idan mun tantance manufar neman ci gaba ta kungiyar kasashen Afirka AU ta ”Ajandar 2063”, da shirin hadin gwiwa da kasashen Afirka da Sin suka samar tare, za mu iya hasashen wasu bangarorin da za a lura da su a taro na wannan karo:
Na farko, a fannin samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa, za a taimaki kasashen Afirka wajen cimma burinsu na zamanantarwa ta fuskar aikin gona.
Yanzu haka kungiyar AU ta sanya burin samun matsakaiciyar karuwar darajar amfanin gonar da za a samar ta 4% a kowace shekara, da takaita yawan hatsin da ake shigowa da su daga ketare zuwa kasa da kashi 40% cikin dukkan hatsin da kasashen Afirka suke samu. Dangane da wannan bukata, fasahohin aikin gona na Sin za su ci gaba da taka rawar gani. Hakika fasahohin noma fiye da 300 da kasar Sin ta yayata a dimbin wurare dake nahiyar Afirka cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, sun riga sun haifar da karuwar amfanin gonar da ake samu ta kashi 30% zuwa 60%.
Na biyu, za a ci gaba da kokarin taimakawa kasashen Afirka cike gibi na fannin kayayykin more rayuwa. Tabbas za a lura da burikan da kasashen Afirka suka sanya na gina cikakken tsarin hanyoyin mota, da na layin dogo a nahiyarsu, da samun wata kasuwar bai daya ta fuskar fasahar dijital. Musamman ma a fannin tattalin arziki na dijital, hukumar ciniki da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya UNCTAD ta nuna cewa, zuwa shekarar 2025, tattalin arziki na dijital zai haifar da karuwar GDP ta dalar Amurka biliyan 180 a nahiyar Afirka, da samar da guraben aikin yi ga miliyoyin matasa. Dangane da batun nan, kasar Sin za ta iya samar da taimako na fasaha da kudi, gami da horaswa, bisa la’akari da matsayinta na wacce ke kan gaba a fannin tattalin arziki na dijital.
Sa’an nan, na uku, a fannin ciniki, kungiyar AU na neman daga yawan cinikin da ake yi tsakanin kasashen Afirka, zuwa kashi 30% na daukacin cinikayyar nahiyar, daga kashi 13% na yanzu. Kana, duk da cewa adadin cinikin da aka yi tsakanin bangarorin Sin da Afirka a shekarar 2023 ya kai dalar Amurka biliyan 282.1, amma bai kai kashi 5% na adadin cinikin Sin da kasashen waje ba. Yayin da darajar cinikayyar da kasashen Afirka suke yi tare da abokan hulda dake waje da nahiyar Afirka, ita ma ba ta kai kashi 3% na darajar cinikin kasa da kasa na duk fadin duniya ba. Saboda haka, ko a fannin cinikayya a tsakanin kasashen Afirka, ko kuma a fannin cinikayya da kasashen dake waje da nahiyar Afirka, dukkansu za a iya inganta su sosai, inda kasar Sin za ta iya ba da taimako, ta hanyar ci gaba da taimakon gina yankin ciniki mai ‘yanci na nahiyar Afirka, da daukar matakan ba da gatanci, da dai sauransu.
Na hudu, shi ne, a fannin neman ci gaba bisa tushen kare muhalli, kasashen Afirka za su iya samun ci gaban tattalin arziki cikin matukar sauri, illa dai ta yi amfani da dimbin albarkatun makamashi da ake sabuntawa, da ma’adinai nau’ika iri-iri masu muhimmanci, da bukatun da ake samu a fannin sauyawar tsarin makamashi, yadda ya kamata. Yayin da kasar Sin, a nata bangare, za ta iya ba da taimako, bisa fifikonta a fannonin kudi, da fasaha, da cikakken tsarinta na masana’antu.
Mun san kasar Sin da kasashen Afirka suna da buri iri daya, wato neman ci gaban tattalin arziki. Kana suna bukatar juna, ta la’akari da tsare-tsaren tattalin arzikinsu. Saboda haka, za a iya gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin Sin da Afirka a dimbin fannoni, wadanda da wuya a yi bayani kan dukkansu cikin makala daya. Amma ya kamata mu san cewa, tunanin ”kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka” zai tabbatar da cewa, kasar Sin ba za ta bar kasashen Afirka cikin hasara ba, kana tabbas taron koli na wannan karo zai haifar da dimbin sakamako masu armashi. (Bello Wang)