Jami’an tsaro a Jihar Sakkwato, sun bayyana cewar wasu ‘yan bindiga daga kasar Mali da suka tsallako iyaka daga Nijar sun kashe mutane 17 ciki har da jami’an sabuwar rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta Kafa guda biyar.
Hare-haren dai sun faru a karamar hukumar Gudu mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.
- Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Kashi 81.69 Cikin Dari Na Masu Bayyana Ra’ayoyinsu Sun Nuna Damuwa Matuka Game Da Karfafa Alakar Soji Tsakanin Japan Da Amurka
- DA DUMI-DUMI: ‘Yansanda Sun Daƙile Harin Bom a Legas
Kantoman karamar hukumar, Umar Maikano Ballee ya shaida wa manema labarai cewa hare-haren na ‘yan bindigar da ake kira lakurawa sun fara ne daga ranar Asabar.
A cewarsa sun kai hari biyu – garin karfen China, inda suka harbi manoma shida har guda hudu suka mutu nan take sai biyu da ke jinya a asibiti, guda a cikinsu rai ya yi halinsa a ranar Talata.
“Bayan kwana daya suka sake zuwa karfen sarki suka kashe mutum takwas, cikinsu akwai jami’an tsaron al’umma, da sauran mutanen gari hudu.” in ji shi.
Kantoman ya kara da cewa suna zargin lakurawa masu shigowa daga Mali da kai hare-haren biyu.
“Sun shigo yankin ranar Alhamis da karfe shida na yamma, sun shigo ta gefen jimajimi, daga nan suka zo suka tsallaka wannan titin na kurdula suka tsallaka nan garin Jeji suka tsallaka kokotau suka tsallaka wannan dajin na karfen sarki.” kamar yadda ya bayyana.
Ya ce ba shi da masaniya kan abin da ya hada lakurawan da mutanen garuruwan sai dai ya ce “abin da muka sani sun zo wadannan kauyuka suna kora shanun mutane, a kwana na biyu sai suka shiga suna harbin manoma.”
Balle, ya ce akwai jami’an tsaro da ke kare jama’a sai dai a ranar da lamarin ya faru, an yi ruwan sama, abin da ya kawo cikas ga jami’an tsaron su kai ga kauyuka a motocinsu.