Bayan dogon nazari kan halin da ake ciki a Jihar Kano sakamakon Zanga-Zangar ƙada baki ɗaya, hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta bayar da umarnin dakatar da duk wani jadawalin karatu da aka tsara nan take. Da zarar komai ya daidaita, za a ci gaba da duk wasu ayyukan ilimi da na gudanarwa cikin tsari kamar yadda aka shirya.
Cikin wata sanarwar da Lamara Garba, mataimakin maga takarda da harkokin Jama’a, an ba da shawarar ga ɗalibai da mazauna cikin harabar jami’ar da su kasance cikin nutsuwa da bin doka, an yi tanadi mai kyau domin tabbatar da tsaron su.
- Jami’ar Bayero Ta Fito Da Kurakuran Da Ake Tafkawa A Rediyo Da Talabijin
- Zanga-zanga: Majalisar Tsaro Ta Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 24 A Kaduna
Hukumar tana mai yin cikakken shiri musamman don bayar da tsaron rayuka da dukiyoyi, don haka tana jawo hankalin mambobin al’ummar jami’ar da su yi taka-tsan-tsan da yawan fita waje don kauce wa duk wani haɗari mai yiwuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp