Kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa ta bayyana cewa, karacin man fetur da ake fuskanta a ‘yan tsakanin nan ya faru ne sakamakon dakatar da dakon man da aka yi saboda kaucewa asara a sanadiyar zanga zangar tsafar rayuwa da ake yi a fadin tarayyar Nijeriya.
Jihohi da dama ciki har da babban birnin tarayya sun fuskanci karancin mai abin da ya haifar da layukan ababben hawa a gidajen man feutur a tsakanin mako biyu zuwa uku da suka wuce, inda hukumar NNPCL ta dora alhakin a kan wasu matsaloli da za a iya shawo kansu ba tare da wahala ba.
- Kwale-Kwale Ya Kife Da Fasinjoji 20 A Jigawa
- DSS Ta Musanta Kai Samame Ofishin NLC Kan Zanga-zangar Yunwa
Yayin da kamfanin NNPCL da masu ruwa da tsaki suka hada hannu don kawo karshen matsalar sai kuma ga zanga-zangar tsadar rayuwa da aka fara ranar Alhamis 1 ga watan Agusta ya sake dagula lamarin har ya haifar da layukan motoci a gidajen mai a wasu jihohin.
Jami’in watsa labarai na kasa na kungiyar masu dakon man fetur, Chif Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa, an ba gidajen mai shawarar su kulle gidajen man ne domin a kaucewa asarar dukiya.
Ya kara da cewa, motocin dakon mai da dama ba su yi dakon mai ba a ranar farko da rana ta biyu ta zang- zangar, wanda hakan ne ya kawo cikas yadda ake aikewa da man fetur din abin da kuma ya haifar da karancinsa a sassan kasa.
“Duk da cewa, shugaban kungiyar, Abubakar Maigandi, ya nemi dillalenmai su ci gaba da harkokinsu amma jami’an tsaro ne da kansu suka bukaci mu dakata saboda yadda lamarin tsaron ta fara tabarbarewa sakamakon zanga-zangar” in ji shi.
A halin yanzu jihohi da dama suna fuskantar karancin man fetur, sun kuma hada da Legas, Abuja, Katsina, da Delta, kamar yadda wakilanmu suka ruwaito mana a ranar Litinin.
Duk da zanga-zangar da ta mamaye sassan kasa, ‘yan bunburutu na ci gaba da cin karensu babu babbaka.