Kungiyar wasan ninkaya ta kasa da kasa ta ba da labarin cewa, tun daga watan Jarairun bana, matsakaicin yawan bincike da mabambantan hukumomin yaki da shan maganin kara kuzari suka yi wa ko wane ‘dan wasan ninkaya na kasar Sin ya kai sau 21, yayin da adadin bai wuce sau 6 kacal ga ‘yan wasan Amurka ba.
Ban da wannan kuma, sau da dama ‘yan wasan Amurka sun fuskanci matsalar amfani da maganin kara kuzari, amma hukumar yaki da shan maganin kara kuzari ta Amurka ta amince irin wadannan ‘yan wasa su ci gaba da shiga gasanni daban-daban bisa wasu hujjoji.
- Hukuma: Ba A Samu Kasar Sin Da Laifin Shan Kwayar Kara Kuzari A Gasar Olympics Ta Paris Ba
- Hukuma: Ba A Samu Kasar Sin Da Laifin Shan Kwayar Kara Kuzari A Gasar Olympics Ta Paris Ba
Baya ga haka, kafofin yada labarai da wasu hukumomi na Amurka, sun dora laifi kan wasu ‘yan wasa bisa wannan batu, don samun damar kai karar su ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC, da kungiyar yaki da amfani da maganin kara kuzari ta duniya wato WADA, da nufin siyasantar da wannan batu, tare da mai da shi wani makami na matsin lamba ga sauran kasashe.
Wasan motsa jiki wanii fanni ne na takara mai muhimmanci ga kasashen duniya, shi ya sa Amurka ta yi kunnen uwar shegu kan abun dake faruwa a cikin gidanta, take kuma matsin lamba kan sauran kasashe game da wannan batu.
Amma, abun lura shi ne Amurka ba ‘yar sandan yaki da amfani da maganin kara kuzari ga ‘yan wasa ta duniya ba ce, kuma ita kadai ba za ta zama sarauniya mai fada a ji a bangaren wasan motsa jiki ba. Dole ne Amurka ta bi ka’idar adalci, da daidaito da yin komai a bayyane. Kana ta rika mutunta shawarar da kungiyoyin kasa da kasa suka yanke, ta yadda za a gudanar da harkokin wasan motsa jiki a duniya yadda ya kamata.
Idan da gaske ne Amurka tana daukar batun yaki da amfani da maganin kara kuzari da muhimmanci, to ya kamata ta daidaita kurakurai da ‘yan wasanninta ke yi a wannan fanni, da biya kudin karo-karo da ake bukata domin tafiyar da harkokin hukumar WADA yadda ya kamata. (Mai zane da rubutu: MINA)