Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da takwararsa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun fara cacar baki kan zaben shekarar 2023.
Lokacin da PDP ta tsaya a kan bakanta na bayyana cewa Tinubu ya ci amanar jam’iyyarsa a 2007, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya bayyana cewa Atiku shi ne babban wanda ya ci amanar ‘yan Nijeriya wajen saba alkawan yarjejeniyar mulkin karba-karba tsakanin yankin arewaci da kuma kudancin Nijeriya.
Cacar bakin dai ta fara kunno kai ne tun lokacin da Atiku ya zargi Tinubu na rashin goyon bayan jam’iyyar ACN a zaben shugaban kasa na 2007, saboda kin amincewa da akidarsa na yin takara tsakanin musulmi da musulmi.
Atiku dai ya kasance shi ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a wancen lokaci, ya bayyana cewa Tinubu ya goyi bayan PDP a zaben 2007, bayan da shi Atiku ya tankwara a niyar tsohon gwamnan Jihar Legas na zama mataimakin shugaban kasa.
Dan takarar jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne lokacin wani shirin safe na gidan talabijin din Arise, inda ya ce takarar shugaban kasa tsakanin musulmi da musulmi ita ce babban matsalar da ta hada shi fada da Tinubu tun a 2007.
Tinubu shi ne ya kafa rushasshiyar jam’iyyar ACN jam kadan bayan da faduwar AD a cikin harkokin siyasa.
Yayin da Atiku ya kasance musulmi daga yankin arewa maso gabas, shi kuma Tinubu musulmi ne da ya fito daga yankin kudu maso yammacin Nijeriya.
A daidai lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu ya zabi Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno a matsayin abokin takararsa, wanda aka samu ce-ce-ku-ce daga wurin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kin amincewa a wurin kungiyar kistoci sakamakon tikitin addini daya.
Da yake mayar da martani kan zabin da Tinubu na tsayar da musulmi abokin takararsa, Atiku ya ce sun dade suna kai ruwa-rana kan wannan matsalar da dan takarar shugaban kasa na APC, amma duk da haka su abokai ne.
Dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce, “Babban matsalar da muka fara samu tsakanina da Tinubu a 2007 shi ne, batun tikitin takarar musulmi da musulmi.
A baya na fice daga ne saboda batun mulkin karba-karba, inda muka kafa ACN tare da Tinubu.
“Tinubu ya so ya kasance abokin takarana lokacin da aka ba ni takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a 2007, amma sai na ki yarda. Saboda haka ne ya goyi bayan Marigayi Umar Yaradua. Wannan shi ne farkon rabuwar kan da muka samu.
“Na dade ina kin amincewa da tikitin takarar musulmi da musulmi, domin kuwa akwai dimbin kabilu da addinai a Nijeriya, wanda ya kamata a samu daidaiton addinai a tsakaninmu.
Har yanzu mu abokanai ne, amma hakan bai hana mu samun rarrabuwar kai a cikin harkokin siyasa ba. Mun fara samun bambancin siyasa ne tun lokacin da muka kasance abokai.”
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na APC ya bayyana cewa akwai shaidu da ke nuna yadda Atiku ya dage wajen yaudarar ‘yan Nijeriya kan tikitin takarar shugaban kasa na musulmi da musulmi.
A cikin wata nasarwa da tsohon gwamnan Jihar Legas ya fitar a yammacin ranar Asabar wanda mai magana da yawunsa, Tunde Rahman ya rattaba hannu ya ce,
Atiku ya yi masa alkawarin mataimaki a 2007, amma daga baya ya kasa cika wannan alkawari kamar yadda a yanzu ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
A cewasa, tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara yin amfani da irin yaudarar da ya saba na yi wa Wike alkawarin mataimakin shugaban kasa bayan gudanar da zaben fid da gwani na PDP amma ya kasa cikawa.
A game da sukar da tsohon mataimakin shugaban kasa yake yi na tikitin takarar shugaban kasa tsakanin musulmi da musulmi, Tinubu ya tunatar da Atiku cewa, ya yi yakin zama mataimakin Marigari Cif MKO Abiola a 1993, bayan da marigayin ya rasa samun tikitin takarar shugaban kasa.
Dan takarar APC ya ce ya kamata duk dan Nijeriya ya yi watsi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, domin yana yunkurin kawo rarrabuwar kai wajen samun nasarar lashe zabe, wanda yake amfani da bambancin addini.
Shi ma daraktan watsa labarai na yakin neman zaben Tinubu, Bayo Onanuga ya mayar da martani kan tattaunawar da Atiku ya yi yana mai cewa, ya kadu lokacin da ya ji Atiku yana ta zuba karya.
Onanuga ya ce Atiku ya bayyana kansa a matsayin wanda ba zai iya gudanar da kyakkyawan shugabanci ba, sannan kuma ya kasance mutumin da ba za a iya amincewa da shi ba wajen danka masa ragamar shugabancin kasar nan.