Koyarwa wata kimiyya ce da take da mafarinta da kuma dokokinta, ana kuma iya lura da su, aunawa,a sake duba yadda lamarinta yake daganan abubuwan da aka karu dasu an koye su ke nan.
Samun hazikin malami wajen da yake amfani da dabarun koyarwa hakan ya kan kai ga samar da bunkasar ilimin al’umma,da abin ya hada da nau’oin bincike.Shirin malami na inganta da bunkasa al’umma ta luggar koyarwa har ila yau kuma akwai bunkasa zumunta tsakanin mamba na sashe da kuma dalibi.Sai dai kuma yawan canje- canjen da ake samu a lamarin da ya shafi ilimin al’umma, idan ana maganar yadda yake inganta ilimi kan sa, har ila yau malmai ya fuskanci matsala, kamar dai yadda malami ya saba da dukkan cikakkun lamurran da cigaba.
- Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Na Duniya Da Rahoto Gaskiya Kan Nijeriya
- Ma’aikatar Tsaron Gidan Kasar Sin: Amurka Na Yunkurin Nuna Fin Karfinta Bisa Amfani Da Makamashin Nukiliya
Don haka ba kamar yadda aka yi tsammani bane a rika ganin ilimin da dalibi ya samu a yi tsammanin ya ishe yin abubuwan da yake bukatar yi ke nan, sai dai samarwa shi dalbin dabarun da zai koyi cigaba da samun sabbin abubuwa wannan kuma ta kokarin da yayi da kan shi ne. Abinda ake bukata mai kuma muhimmanci daga dalibi shine ya koyi yadda zai rika yin tunani da kansa a kimiyyance, mai amfani, dogaro da kan shi, da hanyoyoin da suka dace da yanayi irin na shi. Shi yasa yawancin masu bincike sun maida hankalinsu kan irin wannan yanayin.
Dangane da dabarun koyarwa babu wani abin damuwa kan kokarin da ake yi saboda yawan yin lacca bisa ga la’akarin karuwar dalibai ba.
Dabarun ba su da wani tasiri domin kuwa domin basu nuna hanyoyin da abin ya kasance da kuma dakin karatu, basu kuma taimakawa yadda mutum zai ilimantar da kan shi,da kuma samar da shigo da dabaru.Shi malami an bar shi ne kawai ga fadawa dalibai da kuma karanta wani dan takaitaccen rubutu,wannan kuma ya hada da samo ta yadda zai koya(Al-Nuaimi,2012).An fadi cewa koyarwa an hada ta, ta yin wasu abubuwa da dokokin da suke taimakawa lamarin koyarwar (Al-Ghamdi, 2018).
Don haka koyarwa wata hanya ce da ake zantawa ta abonkantakar zamantakewa, yanayin koyarwar da kuma abubuwan ko yadda wanda ake Koyama yake iya ganewa,wanda a ciki yana da gudunmawar da yake badawa,dole ne kuma a wajen jawabin da za ayi daga karshe na sakamako,wanda shi da ake koyamawa yana koyo da ta fahimta (Ahmed, 2005).
Dabarun koyarwa
Klafki ya bayyana dabarun koyarwa dabaru ne da kuma hanyoyi na abinda aka shirya aka tsara, daidaituwar kimiyya,shi yasa dabarar da za a shirya da gabatarwa da koyarwa da koyo, (Ahmed, 2005). Yayin da shi Danilob ya bayyana fassarar dabarar koyarwa a matsayin lamarin da sai aka yi tunani, da dalilin yin wani abu domin a aiwatar da wani abu na jan hankalin dalibi,da domin komai ba sai a tabbatar da ilimin da ake koya ma shi ya shiga zuciyarsa da fahimtarsa.
Ta wata fahimtar kuma dabarar koyarwa tana bukatar cigaba da abin na fahimtar juna da jan hankali tsakanin malami da dalibi.Wannan na nufin malami ya shirya yadda lamarin dalibi zai kasance ta hanyar darasin da zai koya ma shi.
Ta wancan tsarin ko yin abin, ilimin ya shiga zuciyar dalibin (Ahmed,2005)Shi kuma Knuchel ya fassara dabarar koyarwa da hanyar da zata taimaka a samu nasarar yin mu’amala tsakanin malamai da masu koyo ta yadda za a gane da manufofin ilimin dake cikin darasin da aka koya (Ahmed, 2005).
An fassara dabarar koyarwa a matsayin wasu nau’oin abubuwanko tsare tsaren da malami yake amfani dasu domin samun cimma manufa daga cikin masu koyo.Dabarun koyarwa suna daya daga cikin tsarin koyarwa.Tunanin da ake yi akan lamarin da ya shafi koyarwa bai wuce abinda ake tsammani ba wato zabi, wannan yana nufin zabar daya daga cikin dabarun da ake da su.Amfani da daya daga cikin dabarun yana bukatar daukar mataki daga malami, saboda koyarwa ta kunshi abubuwan da suka zarce ilimin dabarun, saboda shi ilimin malamin da akwai wani abu na lura da hali da abinda ya shafi harshe.
Dabarar koyarwa kadai ba za a iya cewa ta isa ko ta samar da nasara ba. Daya daga cikin ginshikan koyo shine yadda halin malami yake lokacin da yake koyar da dalibansa.Halin da ake ciki yanzu ana kallon dabarun koyarwa a matsayin wasu hanyoyi ne na daidaita yadda za a canza tunani da halin mai koyo da sanin lamuran da ke faruwa a duniya.