Ta yaya za a gane ko wani mutum yana da gaskiya? Ta hanyar gaya masa bukatarka, sa’an nan a duba yadda zai mayar maka da martani. Zai nuna yanayin ko-in-kula, ko kuma zai yi kokarin ba ka amsa mai gamsarwa.
A ranar 12 ga wata, kasar Saliyo, bisa matsayinta na kasar dake shugabantar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na karba karba, ta shirya wani taron muhawara, don tattauna batun kara kujerun kasashen Afirka cikin kwamitin sulhun.
- Xi Ya Yabawa ‘Yan Wasan Olympics Na Sin Da Suka Samarwa Kasar Daukaka
- Peng Liyuan Ta Gana Da Uwar Gidan Shugaban Vietnam
Yayin da yake jawabi, shugaban kasar Saliyo Julius Bio ya ce, har yanzu babu wata kujerar din-din-din ta nahiyar Afirka a kwamitin, kana babu isassun kujeru wadanda ba na din-din-din ba mallakar kasashen Afirka, lamarin da a cewarsa ya nuna rashin adalci irin na tarihi.
A nata bangare, Sithembile Mbete, wata masaniyar ilimin siyasa ta kasar Afirka ta Kudu, ita ma ta ba da jawabi wajen taron, inda ya yi karin tsokaci kan batun rashin adalci da kasashen Afirka ke fuskanta. A cewarta, asalin rashin adalcin shi ne cinikin bayi da kasashen yamma suka kwashe shekaru 400 suna yi, da yadda kasashen Turai da kasar Amurka suka kasa nahiyar Afirka zuwa yankunan mulkin mallaka daban daban, a wani taron da suka gudanar a birnin Berlin na kasar Jamus a shekarar 1884.
Abin lura shi ne, dangane da jawaban da wakilan kasashen Afirka suka yi, wadanda suka nuna rashin jin dadinsu, game da rashin adalci da aka yi musu, kasar Amurka ta nuna yanayin ko-in-kula, ko da yake ta taba halarta da cin moriyar cinikin bayi, gami da kasancewarsa a teburin tattaunawar taron Berlin na shekarar 1884. Yayin da wakiliyar kasar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ke ba da jawabi, ta ambaci maganar da shugaban kasarta Joseph Biden ya yi, ta “nuna goyon baya ga Afirka, da Latin Amurka, da kasashen Caribbeans kan batun neman kujerun din-din-din a kwamitin sulhun MDD” kadai, ba tare da tabo maganar rashin adalci da Afirka ke fuskanta ba, balle ma tuba kan laifukan da kasar Amurka ta taba aikatawa.
A dai wajen wannan taro, dangane da bukatar kasashen Afirka, ta yaya kasar Sin ta mayar da martani? A cikin jawabinsa, wakilin Sin a MDD Fu Cong ya nuna goyon baya ga nahiyar Afirka, inda ya yi Allah wadai da cin zarafin al’ummun nahiyar Afirka da kasashen yamma suka yi a tarihi, da bayyana matakan da suka dauka a matsayin asalin rashin adalci dake damun kasashen Afirka. Kana ya ce har yanzu wannan yanayi na rashin adalci na ci gaba, ganin yadda wasu kasashen yamma ke tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afirka, da neman cin zarafi da sarrafa su.
Daga baya, Fu Cong ya ba da shawara kan matakan da ya kamata a dauka, don daidaita yanayin rashin adalci dake damun kasahen Afirka. A cewarsa, da farko, ya kamata kasashen yamma su daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afirka, da mayar wa jama’ar kasashen Afirka cikakken ikon kula da kai, da tabbatar da makomar kai.
Na biyu, a taimaki kasashen Afirka a kokarinsu na samun ci gaba mai dorewa, da raya masana’antu, da zamanantarwa.
Na uku, a tabbatar da samun dimbin bangarori masu fada a ji a duniya, da nuna cikakken goyon baya ga kasashen Afirka, kan bukatarsu ta yin gyare-gyare kan tsarin kwamitin sulhun MDD.
Kana na hudu, a gyara tsarin hada-hadar kudi ta duniya, don samar da karin tallafi ga kasashen Afirka, da kawo karshen matakin wasu kasashe na yin amfani da manufar kudin su wajen kwace dukiyoyin da jama’ar kasashen Afirka suka tattara.
A zahiri kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka, har ma ta samar da shawarwari masu amfani. Idan ka san manufofin kasar Sin, to, za ka gane duk wadannan shawarwari na cikin manufofin kasar na dogon lokaci.
Idan mun kalli taron kwamitin sulhun MDD da ya gudana a matsayin wata jarrabawa kan cewar “ko ana nuna gaskiya da sahihanci ga kasashen Afirka”, to, na san kasar Sin ta ci jarrabawar. (Bello Wang)