Allah ya albarkanci Nijeriya da lokuta biyu na yin noma, wato lokacin rani da kuma damina; wanda a lokacin damina kamar yadda aka saba, ana fara samun ruwan sama ne daga watan Afrilu zuwa na Oktoba.
Hakan, na bai wa manoma damar yin shuka tare da girbe nau’ikan amfanin gonan da suka shuka.
- An Samar Da Naira Biliyan 2.5 Don Bunkasa Ma’adanai A Nijeriya
- Zaben Shugabanni: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A PDP
Manyan amfanin gonar da aka fi nomawa a kakar damina sun hada da; Masara, Shinkafa, Kubewa, Kankana, Tumatir, Tattasai da kuma Rogo.
1- Masara: Ta kasance daya daga cikin manyan amfanin gona a Nijeriya da ake nomawa a lokacin rani, wadda kuma ake sarrafawa zuwa nau’ikan abinci daban-daban.
Ya fi kyau a shuka Irinta daga watan Afirilu zuwa na Mayu, duba da cewa lokacin ne a ake fara samun mamakon ruwan sama.
Yana da kyau a sani cewa, Masara na bukatar ingantacciyar kasar noma mai kyau tare da danshi mai yawa; sannan dole ne a kula da cire mata Ciyawa, domin ta samu ta girma cikin sauri.
2- Shinkafa: Ita ma na daya daga cikin manyan amfanin gona a Nijeriya, wadda ake shuka Irinta da damina; ana kuma sarrafa nau’ikan abinci ir-iri da ita. Kazalika, ya fi dacewa a shuka Irinta daga watan Afrilu zuwa na Yuli, musamman ganin cewa; a lokacin ne ake samun ruwan sama mai yawan gaske.
Haka zalika, Shinkafa na bukatar a yi mata gyaran gona kafin a shuka Irinta tare da cire mata Ciyawa, don ta samu damar girma da sauri.
3- Kubewa: Ita ma na daya daga cikin kayan lambun da ake nomawa da damina, sannan kuma tana dauke da sinadarin da ke gina jikin Dan’adam.
Kazalika, ta fi dacewa a shuka Irinta daga watan Afrilu zuwa na Yuli; duba da cewa a cikin wadannan watanni ne aka fi samun mamakon ruwan sama.
Har wa yau kuma, tana bukatar kasar noma mai kyau tare da yawan cire mata Ciyawa; don a samu ta yi girma da wuri.
4 Kankana: Ita ma a Nijeriya, ana bukatar a shuka Irinta a lokacin damina; kamar yadda aka sani ne kuma tana dauke da sinadarin da ke gina jikin Dan’adam, ana kuma sarrafa ta zuwa nau’ika daban-daban.
Akasari, an fi shuka Irinta ne daga watan Afrilu zuwa na Mayu; sannan kuma ana bukatar a yi mata gyaran gona kafin a shuka Irinta tare da cire mata Ciyawa, don ta girma da wuri.
5- Tumatir: Yana daya daga cikin kayan lambu da ake shuka Irinsa a Nijeriya a lokacin damina, wanda kuma ya fi kyau a shuka Irinsa daga watan Afrilu zuwa na Mayu tare kuma da shuka Irinsa a kasar noma mai kyau da cira masa Ciyawa, don a samu ya girma da wuri.
6- Tattasai: Shi ma ya kasance daya daga cikin kayan lambun da ake shuka Irinsa a Nijeriya, musamman a lokacin damnina. An fi so a shuka Irinsa daga watan Afrilu zuwa na Mayu, kazalika kuma yana bukatar kasar noma mai kyau tare da danshi, sannan dole a kula da cire masa Ciyawa, domin ya girma da wuri.
7- Rogo: Shi ma ana shuka Irinsa a Nijeriya a lokacin damnina, sannan kuma ana sarrafa shi zuwa nau’ikan abinci daban-daban.
Mafi akasari, an fi bukatar a shuka Irinsa daga watan Afrilu zuwa na Yuni, kana kuma yana bukatar ingantacciyar kasar noma da kuma waje mai matukar danshi, don ya girma da wuri.