Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shiga tsaka mai wuya bayan da ‘yan wasanta guda biyu, Martin Ordigaard da Ricardo Callafiori suka samu rauni a wasannin da suka bugawa kasashensu na wasannin gasar cin kofin Nations League.
Sannan a wasan kungiyar da Brighton, an ba wa dan wasan Ingila, Declan Rice jan kati, wanda hakan ya sa kungiyar ta tashi wasan 1-1 a filin wasa na Fly Emirates dake birnin landan, kafin a tafi hutun wasannin kasashe. Sannan wani kwamiti mai zaman kansa da ke kula da yanayin alkalanci a gasar Firimiyar Ingila ya ce jan katin da alkalin wasa Chris Kabanagh ya ba wa Rice ya dace kuma kwamitin da yake bitar yadda aka busa wasannin babbar gasar ta Ingila a duk mako, ya ce ya dace da aka kori Rice daga karawar.
- Sakon Da Aka Isar Game Da Yanayin Tekun Kudancin Kasar Sin Daga Wasu Taruka Uku
- Ana Iya Ganin Sabon Karfin Sin A Bikin Baje Kolin CIFTIS
Tun farko an bai wa Rice katin gargadi, sai ya taba kwallo a lokacin da Joel Beltman zai yi bugun tazara a minti na 49 kuma lamarin ya faru ne a wasan Premier League mako na uku da suka tashi 1-1 tsakanin Arsenal da Brighton a Emirates ranar Asabar 31 ga watan Agusta.
Shi ne jan katin farko da aka ba wa Rice a tarihinsa, inda kwamitin ya ce yana sane ya taba kwallon, kenan hukuncin ya dace da shi, wanda tun farko yana da kati mai ruwan dorawa wanda ya samu ana tsaka da fafatawar.
Kwamitin mai zaman kansa ya kunshi tsofaffi uku ko dai ‘yan wasa ko masu horarwa da wakili daga Premier League da wani daga masu alkalancin gasar haka kuma kwamitin ya ce BAR ta yi daidai da hukuncin da ta yanke a kwallon da Trent Aledander-Arnold ya ci a wasan da Liberpool ta ci Manchester United 3-0 a Old Trafford.
Sai dai kungiyar Arsenal za ta buga wasa biyar cikin Satumba da ya hada da uku a Premier League da Champions League da kuma League Cup inda Tottenham za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan hamayya karawar mako na hudu a Premier League ranar 15 ga watan Satumba.
Kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dan wasa Martin Ordegaard ya samu rauni a lokacin da yake wakiltar kasarsa ta Norway, sannan shima Ricardo Callafiori ya samu ciwo a lokacin da yake bugawa kasar Italiya wasa da Faransa.
Hakan yana nufin watakila Arsenal za ta buga wasan Tottenham ba tare da ‘yan wasa Ordegaard da Callafiori ba sannan dan wasa Declan Rice ma ba zai buga wasan ba saboda jan katin da aka bashi a wasan Brighton.
Haka kuma Arsenal za ta je Italiya domin karawa da Atalanta a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba kuma wannan shi ne karon farko da Atalanta da Arsenal za su kece raini a babbar gasar ta Zakarun Turai a tsakaninsu.
Wasa na uku da Arsenal za ta yi a waje a jere a Satumba, shi ne a gidan Manchester City a mako na biyar a Premier League ranar 22 ga watan Satumba daga nan ne kuma Arsenal za ta karbi bakuncin Bolton a League Cup da za su kece raini a Emirates ranar 25 ga watan Satumba.
Wasa na karshe da Arsenal za ta yi a cikin watan Satumba, shi ne wanda Leicester City za ta je Emirates a mako na shida a babbar gasar ta Ingila ranar 28 ga watan Satumba. Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier League da maki bakwai, bayan da ta ci wasa biyu da canjaras daya.
Wasannin da Arsenal za ta kara cikin Satumbar Premier League ranar Lahadi 15 ga watan Satumba
Tottenham da Arsenal Kofin Nahiyar Turai ranar Alhamis 19 ga watan Satumba
Atalanta da Arsenal Kofin Premier ranar Lahadi 22 ga watan Satumba. Man City da Arsenal League Cup ranar Laraba 25 ga watan Satumba Arsenal da Bolton Kofin Premier ranar Asabar 28 ga watan Satumba Arsenal da Leicester.