Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya rushe daukacin shugabannin rikon kananan hukumomin Jihar Kano 44.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Laraba, inda hakan ya kawo karshen wa’adin kantomonin na watanni shida da suka kwashe suna jagorantar harkokin kananan hukumomin Jihar.
- Yawan Mutanen Da Suka Shiga Da Fita Daga Kasar Sin A Hutun Bikin Tsakiyar Kaka Ya Zarce Miliyan 5.25
- Kotu Ta Sanya Rana Kan Batun Tsige Ganduje A Matsayin Shugaban APC
Kamar yadda sanarwar ta tabbatar da umarnin da aka bai wa shugabannin rikon kananan hukumomin, cewa su mika harkokin gudanarwar ayyukan kananan hukumomin ga daraktocin gudanarwar kananan hukumomin su.
Idan za’a tuna dai, a zaman majalisar dokokin Kano na ranar Litinin din da ta gabata, an gabatar da bukatar karin watannin biyu ga shugabannin rikon, wanda kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin Jihar ya kalubalanci wannan kudirin, har sai da takai ga zazzafar mahawara da ta janyo shugaban marasa rinjaye ficewa daga zauren majalisar.