Dubun wani tsoho dan shekara 74 mai suna Jibrin Musa mazauni a gudunmar Rigasa ta Karamar Hukumar Igabi da ke a Jihar Kaduna ta cika, biyo bayan kama shi da aka yi yana satar Tabarmar wani Masallacin unguwa da ke yankin.
Jibrin wanda yake da zama a layin Turaki da ke a yankin. An kama shi ne, bisa zargin satar Tabarma a wani Masallaci da ke a layin Sarkin Bori Sule da ke a yankin.
- Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Danyen Aikin Dake Barazanar Jefa Yankin Cikin Wani Bala’i
- 2027: Majar Atiku Da Obi Da Kwankwaso Ta Fada Shakku
A hirarsa da wakilinmu, jim kadan bayan kama shi, tsohon ya ce, “ Ba zargi bane, tun da an kama ni na saci Tabarmar, ” in ji shi.
Ya ce, “Na shafe shekaru goma ina satar sabbin shinfidun Sallah a masallatai daban daban da ke a yankin da Agon Bango na masallatai, amma ban cika yawan satar Alkur’anai a masallatai ba ”.
Ya ci gaba da cewa,“ Na kan shiga cikin mallatai ne in yi satar kamar idan an idar da ko dai Sallar Azahar ko ta La’sar, wani lokacin ma da ni ake yin Sallar, sai in sace sabbin tabarmin in sanya a cikin babbar Leda in boye su a cikin babbar Rigar da nake sanye da ita, in fice daga masallacin in je in sayar da su”.
Ya kara da cewa,“ Na kan sayar da kowacce daya daga Naira 1,500 zuwa Naira 2,000, wannan shi ne karo na biyu da na saci tabarma a wannan masallacin”.
Daya daga cikin ‘yan kwamitin Masallacin Miftahu Ibrahim ya shaida wa LEADERSHIP Hausa yadda su kama kama tsohon, inda ya ce, “ An dade ana yi mana satar kayayyaki a Masallacin ciki har da Tabarmin Sallah da sauran wasu kaya”.
“ Na zo Masallacin na bude na share shi aka kuma gabatar da Sallar Azahar, sai ni da wani abokina muka tashi muka fita wajen Masallacin, sai ga tsohon ya shiga cikin Masallacin, can zuwa jimawa kadan ya fito daga cikin Masallacin ya zagaya bayan Masallacin kamar zai kama ruwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Bayan da tsohon ya wuce, sai na leka cikin Masallacin na ga ba wata Tabarma, sai muka bishi a baya, muka ce masa ya dakata, bayan ya dakata sai muka ce masa ina Tabarmarmu da ya dauka a cikin Masallaci, sai ya fito da ita a nade, daga cikin babbar rigarsa”.
Shi ma Na’ibin Masallacin Malam Muhammad Shu’aibu ya shaida wa wakilinmu cewa,” Saboda yawan sace-sacen a Masallacin har ta kai ga a tsakaninmu ‘yan kwamitin Masallacin muna zargin junanmu, da sauran wasu mutanen layin”.
Shi kuwa Mai Anguwar da ke a layin, Malam Aminu Alasan ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, akwai Masallatai da dama a layin da ake korafen-korafen satar kaya a Masallati, inda muka dukufa yin addu’ar sai gashi a kama wannan tsohon.