A yayin da aka fara girbe wasu daga cikin amfanin gonar da manoma suka shuka a kakar noman bana, farashin Tumatir, Tattasai, Doya da kuma Rogo, ya ragu a wasu sassa na cikin wannan kasa, wanda hakan ya samar da saukin tsada ga masu amfani da su.
Wannan na zuwa ne, daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen rashin abinci, wanda hakan ya haifar da matukar tsadar kayan abincin a dukkanin fadin wannan kasa.
Shirin samar da abinci na duniya da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya ruwaito cewa, mutane miliyan 4.4 a shiyyar Arewa maso Gabas, na fuskantar kalubalen rashin abinci mai gina jiki.
Haka zalika, wani bincike da jaridar BusinessDay ta gudanar a wasu kasuwanni da ke Jihar Legas ta gano cewa; farashin Rogo ya ragu da kashi 42.5, inda ake sayar da shi a kan Naira 2,300; sabanin yadda ake sayar da shi a watan Yuli kan farashin Naira 4,000.
Bugu da kari, farashin buhun Rogo mai nauyin kilo 50, ya ragu zuwa Naira 65,000; sabanin yadda ake sayar da shi a watan Yuli kan farashin Naira 75,000.
Kazalika, farashin Dankali ma ya ragu da kashi 50 cikin 100; sakamakon manomansa sun fara girbinsa a jihohin da aka fi noma shi.
Sannan, farashin Tumatir shi ma ya sauka da kashi 58 cikin 100 a Jihar Legas, inda ake sayar da babban kwando a kan Naira 120,000 zuwa Naira 50,000 a kasuwar Mile 12.
A garin Onitsha kuma, babban kwandon Tumatir ana sayar da shi daga Naira 60,000 zuwa Naira 75,000 a kasuwannin Ochanja da kuma Ose.