Limamin cocin ‘Anglican Communion’, Reb Henry Ndukuba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wani sabon kundin tsarin mulkin tarayya wanda zai kasance mai amfani da mutane.
Ndukuba ya yi wannan kiran ne a wurin bude taron kwamitin cocin Nijeriya da ya gudana a cocin ‘St. Andrew’s Basilica Anglican Church’ a Jihar Inugu.
- Rahoto Ya Nuna Yadda Noma Ya Samu Koma-baya A Nijeriya
- Xi Jinping: Inganta Gina Dunkulewar Kabilun Kasar Sin Baki Daya
Limamin cocin a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na cocin, Korede Akintunde ya sanya wa hannu, ya ce kowa ya san cewa Nijeriya na fama da matsaloli da dama, wasu daga cikinsu sun bayyana wanda mabambamtan kungiyoyi suka ankarar, musamman ma na zanga-zangar nuna adawa da rashin shugabanci nagari.
Ya bayyana cewa yayin da majalisar dokokin kasar ta yi aiki mai kyau wajen gyaran kundin tsarin mulkin da aka gada daga sojoji, ya kamata a ce Nijeriya ta samu sabbin dokoki a halin yanzu.
“Wannan sabon kundin tsarin mulki zai yi la’akari da abubuwan da aka riga aka bayyana a tarukan kasa da kuma kiraye-kiraye daban-daban na sake fasalin Nijeriya.
Nisantar wannna ya sa har yanzu ba gano bakin zaren matsalolin kasar nan ba,” in ji shi.
Limamin cocin ya ci gaba da cewa, makama guda daya tilo da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke bukata ta shimfida shi ne, na tabbatar da mulkin dimokuradiyya da kuma bai wa Nijeriya sabon kundin tsarin mulkin farar hula da ya dace da dimokuradiyya wanda zai magance tushen matsalolin ‘yan kasa.
Ya kuma lura da cewa zanga-zangar kyamar rashin shugabanci nagari da aka gudanar duk da rashin jagoranci da manufa ta yi tasiri a wurin gwamnatin tarayya da na jihohi.
“Wannan ya nuna karara cewa jama’a sun gaji da ci gaba da yin alkawurran da gwamnati ta yi na dakile tsadar rayuwa wanda ya haifar da matsananciyar wahala ga magidanta a kasar nan.
“Bugu da kari, kiraye-kirayen da ake yi akai-akai don mahukunta su fahimci halin da ake ciki ko za su sauya salon mulkinsu tare da yin ayyukan da suka makata wajen fitar da al’ummar kasar nan daga kuncin rayuwa.
“Wannan zanga-zangar wani kira ne ga gwamnatoci a dukkan matakai, musamman na tarayya da suka yi kunnen uwar shegu da kukan da jama’a ke yi kan abubuwan da ke ci musu tuwo a karya, domin babu wata gwamnati da za ta iya kafa doka ko hana mutanen da ke fama da yunwa yin zanga-zangar.”
Har ila yau, cocin na Nijeriya ya nuna takaicin yadda wasu masu zanga-zangar suka daga tutocin kasar Rasha a wasu sassan kasar, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, domin ya saba ka’idojin zanga-zangar a Nijeriya, kuma da alama ce ta saba wa tsarin mulki na sauyin gwamnati ba bisa ka’ida ba.
“Mun tabbatar da cewa, wannan hadin gambizar da aka yi ba daidai ba ne, zai iya haifar da rugujewar dimokuradiyyarmu, ya kamata a yi cikakken bincike kan lamarin da magance musabbabin wannan aika-aika da kuma masu ta da zaune tsaye.
“Abin takaici, yana iya yiwuwa akwai alaman tambaya kan wannan lamarin, domin da akwai wata makarkashiya, muna kira da a dauki matakin dakile aukuwar lamarin nan gaba,” in ji shi.
Cocin ta kuma jinjina wa Shugaba Tinubu da ma’aikatan Nijeriya kan rattaba hannu a kan sabon mafi karancin albashi na naira 70,000, inda ta ce wannan abin a yaba ne.
“Duk da haka, muna kira ga gwamnati da ta tsawaita shirinta na biyan ‘yan fansho, wadanda da yawa daga cikinsu na rayuwa ne cikin yunwa, akwai bukatar a sake duba kudaden fansho duk bayan shekaru biyar kamar yadda dokar kasa ta tanada.”
Malamin cocin ya tunatar da masu rike da madafun iko cewa ma’aikatan yau su ne ‘yan fansho na gobe, yayin da ya bukaci majalisar dokokin kasar da tabbatar da biyan kudaden fansho ga wadanda suka cancanta a lokacin da ya kamata.