Rundunar ‘yansandan Jihar Legas, a ranar Talata, ta gurfanar da wata mata mai suna Rukayya Dantata ‘yar shekaru 35 a gaban kuliya bisa zargin damfarar wani kamfanin tuntuba na Bureau de Change kudi Naira miliyan 350,900,000.
An gurfanar da Dantata a gaban kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja da laifuffuka biyu da suka hada da zamba, damfara da kuma karbar kudi ta hanyar karya.
- EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Taraba Ishaku Kan Zargin Badaƙalar 27bn
- Rahoto Ya Nuna Yadda Noma Ya Samu Koma-baya A Nijeriya
Lauyan mai shigar da kara, Ezekiel Rimamsomte, ya shaida wa kotun cewa Dantata ta aikata laifukan da ake zarginsa tsakanin watan Yuli zuwa Agustan 2022.
Ya ce wacce ake kara ta samu Naira miliyan 350,900,000 ta hanyar damfara, inda aka tura ta zuwa asusunta na Zenith Bank, 2082551256, da kuma asusun kamfaninta mai suna Adat Bentures’ mai lamba, 1014937041, da sunan Rukayya Saadina Dantata.
Rimamsomte ta kara da cewa Dantata ta yaudari wadanda masu kudin, Saka Rasak na Rosiyike, da wasu na kamafanin Financial Consultant Ltd, da ke No. 50 Kingsway Building, Legas, ta hanyar yin kamar suna gudanar da harkokin kasuwanci na halal.
A cewarta, laifukan da aka aikata sun ci karo da sashe na 1 (a) (3) na dokar damfara da sauran laifukan da suka shafi doka ta 2006, da sashe na 323 na dokar laifuka ta Jihar Legas 2015.
Sai dai Dantata ya musanta zargin da ake mata.
Igbodo ya bukaci kotun da ta bayar da belin wacce ake tuhuma a karkashin “mafi sassaucin sharuda,” yana mai cewa, “Wanda ake tuhumar ya bi dukkan sammacin ‘yansanda da Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati, kuma ba ta tsallake beli ba, duk da kalubalen lafiyarta.”
Ya kuma shaida wa kotun cewa mijin Dantata, Alhaji Ismaih Singer, da kuma wata Otunba Olutaye Ariyo sun hallara a gaban kotu domin a ba ta belinta.
Mai gabatar da kara bai musanta da neman belin ba kuma ya bar hukuncin ga hukuncin kotun.
A wani takaitaccen hukunci mai shari’a Rahmon Oshodi ya bayar da belin Dantata kan kudi Naira miliyan 30 tare da mutane biyu da za su tsaya mata.
Alkalin ya bayyana cewa, “Dukkanin wadanda za su tsaya mata dole ne su ba da takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku ga gwamnatin Jihar Legas.”
Mai shari’a Oshodi ya kuma umurci Dantata da ta ajiye fasfo dinta da sauran takardun tafiya zuwa ga babban magatakardar kotun, inda ya kara da cewa dole ne magatakardar ta tantance adireshin gidanta da ofishinta.