Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya. A yau shafin namu zai muku bayani akan yadda za ki samu karin ni’ima.
Idan kina neman maganin karin ni’ima da ruwa to kin zo inda za ki samu.
Idan har kina so ruwan dadi da ni’ima su karu a jikin ki yadda za ki birge mijin lokacin saduwa.
Zaki iya zabar hadi daya ki dinga yi kina sha:
Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga ciki:
Ruwan kankana, Ayaba Manya uku, kankana Kwata da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya yi sanyi, ki sha kamar lemo ke da maigida, yanada kyau sosai.
2- Ruwan tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa ki ci, shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da saka jin dadin auratayya, sannan hakan yana saka gogewar fata.
3- Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da magoki, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fid da dusar.
Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya, ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki, ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki barshi ya kwana. Ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, uwargida za ki bada labari.
4- Ruwan Zogale: Amfanin ruwan Zogale ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikinmu ne kawai.
Ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan zogalen ki zuba kanumfari da Citta ki tafasa. Sai ki sauke ki dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya saukar da ni’ima sosai. Ya na kara wa mace kuzari a jikinta sosai, sannan ya na kara wa mace juriya wajen saduwa.
Ki tsinke zogale ki wanke ki markada ganyen a blander ko ki mutsuttsuka da hannunki ki kara ruwa a kai ki tace ki matse dusar ki zuba madarar ruwa gwangwani daya a cikin ruwan zogale ki sa a cikin Jug daya, ki sa zuma ta ji sosai, ki juya ya hadu ki dinga sha. Gaskiya ba shi da dadin sha, sai dai akwai shi da aiki; ni’ima lutsutsu! Domin duk bushewar gabanki da rashin ni’imarki sai ni’ima ta zo, kuma ya na sa jin dadi sosai.
7. Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa, idan ya yi luguf sai ki markada a blander za ki gan shi da kauri kirtif, sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai, idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka.
Bayan awa uku da shan ki za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu da son kasancewa da maigidanki. Za ki ji dadin da ki ka dade ba ki ji ba, maigida kuwa zai gamsu da ke sosai.
6.Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsi-gutsi ki daka a turmi ko ki markada a blander kina yi ki na kara ruwa a dusar raken kina matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasasshen baure jog daya sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog daya.
Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya sai ki sauke amma za ki sa kanumfari da kayan kamshi a dahuwar idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima maigida zai dinga jin gamsuwa da ke sosai. Tsimin rake kenan.