Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Peter Obi, ba ya goyon bayan ‘yan ta’addar (IPOB) da ayyukansu.
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust a shirin siyasa a ranar Litinin.
- Bayan Shafe Shekaru Yana Adawa Da Buhari, Orubebe Ya Koma APC
- Ko Wace Kwarya Tana Da Abokin Burminta
“Ban yarda da cewa Peter Obi yana goyon bayan IPOB ba saboda ba zan kasance tare da shi ba a yau (idan yana goyon bayansu),” in ji shi.
Ya lura cewa wadannan zarge-zarge ba su da wani tushe.
Ya ce, “Irin wannan hirar suka yi da ni lokacin da na ce ina so a tattauna da ni akan zaben 2023 a matsayina na dan Najeriya. Babu wani abu da mutane ba za su iya fada ba. A safiyar yau, dole ne in yi taron manema labarai don yawan labaran karya da ke yawo… wadannan zarge-zargen har yanzu ba su da tushe.”
Baba-Ahmed ya kara da cewa kafin ya amince ya zama abokin takarar Obi, ya yi duk binciken da zai iya kuma babu abin da ya danganta tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyar IPOB.
Ya ce, “Misali, sun ce an yi wa ’yan Arewa rashin adalci ta hanyar sanya katin shaida, kafin na yanke shawarar shiga takara da Peter Obi. A cikin makonni na yi duk binciken da zan iya.
“Kuma ya kamata in zauna in yi imani da mutanen da ba su da hankali suna magana ko ta yaya saboda kun fito siyasa lokacin da na san irin siyasar da muke takawa.”