Bayan an gano danyen mai a 1950 Nijeria ne, aka fara yiwa fannin aikin noma na Nijeriya rkon Sakanr Kashi.
Fannin wanda na daya daga cikin gwagwarmayar da masu hakilon samun yancin kan kasar suka karfafa shi na kan gaba wajen habaka tattalin arzikin kasar.
- Nazari Kan Gazawar Tsofaffin Ministocin Noma 52 Da Suka Shude A Nijeriya
- Jihar Filato Ta Yi Hadaka Da Kasar Bulgeriya A Fannin Noma
Kafin samun ‘yancin kan kasar, a 1950 Nijeriya ce kan gaba a duniya, wajen noma Kwakwar Manja da kuma Cocoa.
Hakazalika, fannin na samar da ayyukan yi da suka kai sama da kashi 70, wanda hakan ya kai kusan kashi 62.3 na kudaden musayar na shiga, da kasar ke samu.
Bisa wata kididdiga da aka samu daga gun bankin duniya ta nuna cewa, fanin na samar da sama da kashi 60, ga tattalin arzikin kasar.
Sai dai, bayan gano danyen man a 1950, hakan ya janyo an yi watsi da fannin, wanda hakan ya sanya kimar Nijeiya a fannin aikin noma a fadin duniya, ta fadi warwas.
Amma domin a sake farfado da kimar Nijeriya a fannin, shugabannin da suka mulki kasar, sun kirkiro da tsare-tsaren aikin noma da ban da ban.
Sai dai, abun takaicin shi ne, wadannan tsare-tsaren, kusan za a iya cewa, ba su wani tasiri ba saboda sauye-sauyen shugabanci da aka samu a kasar.
Tsare-Tsaren Da Aka Kirkiro Bayan Samun ‘Yancin Kai:
Domin rage radadin yakin basasa a fanin aikin noma, tsohuwar gwamnatin mulkin soji ta Janar Yakubu Gowon mai murabus, ya kirkiro da tsarin NAFPP na kasa a 1972 don bunkasa samar da abinci, ta hanyar ilimantar da manoma.
An kaddamar da tsarin na gwaji a jihohin Anambra, Imo, Ondo, Oyo, Ogun, Benue, Filato da Kano.
Sai dai, tsarin ya ci karo da kalubale na rashin gazawar manoma na kafa kungiyoyi don a tallafa masu da kudaden aikin noma da sauran kayan aiki.
Hakazalika,a a 1973, Gowon ya kafa hukumar RBDA bisa nufin samar da kayan aikin noma rani, ta hanyar kakkafa Dam Dam don tara ruwan na noman rani.
Daga baya kuma a 1975ya kirkiro da aikin bunkasa aikin na noma ADP.
Bugu da kari, a lokacin tsohowar gwamnatin mulkin soji ta Cif Olusegun Obasanjo a 1976 bankin CBN, ya kirkiro da aikin habaka aikin noma na kasa OFN.
Manufar ita ce, don a kara yawan noma da ake yi a kasar, musamman don a samar da abinci, mai gina jiki.
Tsarin ya kai har 1979 na lokacin mulikin tsohowar gwamnatin farar hula ta marigayi Shehu Shagari.
A watan Afirilun 1980, Shagari ya kirkiro da tsarin farfado da aikin noma na GRP bisa nufin samar da wadataccen abinci ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
Bugu da kari, a 1986, lokacin tsohuwar mulkin soji ta tsohon shugaban kasa na mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai murabus, ya kirkiro da tsarin DFRRI, bisa nufin tallafa wa alumomi.
Daga 1999 zuwa 2020:
Tsohohuwar gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, a watan Afirilun 2003, ya kirkiro da tsarin aikin samar da wadataccen abinci na kasa NSPFS.
Ya kirkiro da tsarin don a taimaka wa manoma su samun karin kudaden shiga da karfafa ayyukan noman rani da sauransu.
Sai dai, tsarin ya ci karo da matsala saboda manoman da aka bai wa kudin rancen yin noma, sunki maido da kuadaden a kan lokaci tare da kuma kalubalen da manoman suka fuskanta na rashin yin amfani da kimiyyar fasahar noma.
A shekaru takwas na mulkin Obasanjo, fannin ya bayar da gudunamawa na bunkasa tattalin arzikin kasar.
Har ila yau, a lokacin tsohuwar mulkin marigayi shugaban kasa Umaru Yar’Adua, ya kirkiro da tsarin ajanda bakwai da kuma shirin habaka aikin noma na kasa NFSP.
Manufar shirin ya hada da; bayar da kudaden hadaka na aikin noma na FADAMA III; IFAD da ayyuan bunkasa aikin noma na ADB da sauransu.
Yar’Adua, ya bayar da gagarumar gudunmawa ga tattalin arzikin kasar wadda ta kai kashi 25.31.
Bugu da kari, a 2011, tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya kaddamar da tsarin aikin noma na ATA.
Ya kirkiro da tsarin ne, domin a habaka noman, musamman kanaanan manoma wanda kimanin kanannan manoma 45,300 da ke a karkara suka amfana.
A lokacin, fannin ya taimaka da wajen kashi 21.09 ga tattalin arzikin kasar.
Hakazalika, a lokacin mulkin tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin dimokiradayya Muhammadu Buhari a shekarar 2015, ya kirkiro da tsarin habaka aikin noma na APP.