Duk da kalubalen rashin tsaron da Nijeriya ke ci gaba da fuskanta, hukumar kididiga ta kasa (NBS) ta sanar da cewa, zuba hannun jari kai tsaye na kasashen kere a fannin aikin noma, ya karu da kashi 226.45 cikin watanni uku na 2024 a Nijeriya, musamman idan aka kwatanta da zango na 2023.
Rahoton baya na shigo da kaya cikin kasar na hukumar ya nuna cewa, zuba hannun jari na kai tsaye cikin fannin aikin noman a zango na daya na 2024, daga dala miliyan 4.84; yanzu ya kai dala miliyan 15.80 daidai da na zangon farko na 2023.
- Wane Ne Ke Tallafa Wa Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Da Kudade?
- Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo
Haka zalika, daga zango zuwa zango; zuba hannun jari na kai tsaye, ya karu zuwa kashi 3,661.90 a zango na hudu na 2023, wanda ya kai dala miliyan 0.42.
Duk da matsalar ta rashin tsaro da ke hana manoma zuwa noma gonakinsu ta hanyar daukar hayar jam’in tsaro masu zaman kansu, zuba hannun jari na kai tsaye a fannin aikin noman kasar, ya karu matuka tun a zangon farko na 2022.
Wani masani a fannin aikin noma, Africanfarmer Mogaji; ya sanar da cewa, sakamakon gibin da ake da shi na samar da wadaccen abinci a kasar; wasu ‘yan kasashen waje na yin amfani da wannan dama wajen zuba hannun jarinsu a fannin, don samun riba mai yawa.
A cewarsa, “Mu ‘yan Nijeriya, mu ne muke ganin kaluabalen rashin tsaro, amma su ‘yan kasashen wajen na yin amfani da wannan damar suna zuba jarinsu a fannin”.
Ya kara da cewa, zuwa zango na gaba ‘yan ketaren za su kara yin amfani da wannan dama ta kalubalen rashin tsaro a kasar; ta yadda za su kara zuba hannun jarinsu a fannin da yawan gaske.
Ya ci gaba da cewa, a Nijeriya ba a tanadi ingantaccen tsari a fannin aikin noma ba, haka nan ba a kuma samar da kayan aikin noman ingantattu ba, musamman don cike gibin da ake da shi na samar da wadataccen abinci, wanda hakan ke ci gaba da bai wa ‘yan kasar waje damar zuba hannun harinsu a fannin aikin noma na kasar.
Kazalika, ya sanar da cewa; fannin ya taimaka wa tattalin arzikin kasar a zango na daya a 2024 daga kashi 0.18 ya kai har kashi 2.19 a lokaci guda a bara.
Shi ma wani masani a fannin, Ibrahim Tajuddeen ya sanar da cewa; gibin da aka samu da kuma kalubalen da ake ci gaba da fuskanta na rashin tsaro a kasar ne ya haifar da yawan samun ‘yan ketare, suna zuwa suna zuba hannun jarinsu a fannin aikin noman kasar.
A zango na daya na 2024, jimillar kudade na Nijeriya na shigo da kaya ya karu zuwa kashi 198.06, wanda aka kuma samu dala biliyan 1.13 a zango na daya na 2023 zuwa dala biliyan 3.37, duk a wannan lokaci.
An kuma samu karin da ya kai kashi 210.16 daga zango zuwa zango daga dala biliyan 1.08 a zango na hudu na 4 na rubi’in shekarar 2023.